Hukumar Saudiya ta kama mutane 46 kan harin bam a Madina

Hukumar Saudiya ta kama mutane 46 kan harin bam a Madina

- Saudiya ta kama mutane 46 kan harin kunar bakin wake da aka kai a birnin Madina bara

- An dora alhakin harin ne a kan kungiyar IS, wata kungiyar 'yan bindiga

Saudiya ta ce ta kama mutane 46 bayan harin kunar bakin wake da aka kai a birnin Madina bara.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, akasarin mutanen 'yan kasar ta Saudiya ne, amma an ce akwai mutane 14 'yan wasu kasashe da suma a ke tsare da su.

KU KARANTA KUMA: Sheikh Gumi ya ki amince da Sarkin Kano akan ra'ayinsa bisa auren mata masu rashin aiki

Saudiya ta ce mutanen, mambobin wata kungiyar 'yan bindiga ce da ta kai harin, a inda a ka kashe jami'an tsaro 4.

Hukumar Saudiya ta kama mutane 46 kan harin bam a Madina

Harin bam a garin Madina

A lokacin da a ka kai harin, an dora alhakin shi ne a kan kungiyar IS.

Harin ya auku ne a watan Yulin bara, a karshen azumin watan Ramadana.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda sunan Allah ya bayyana a jikin itacen moringa.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel