Na gargaɗi Jonathan kan makircin 'yan Arewa – Inji David Mark

Na gargaɗi Jonathan kan makircin 'yan Arewa – Inji David Mark

- David Mark ya ce ya gargadi tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan kan irin makircin da 'yan arewa ke shirya yi domin kayar da shi a zaben 2015

- Mark ya ce da gangan ne jam'iyyar PDP, a karkashin Adamu Mu'azu ta gaya wa Jonathan cewa zai lashe zaben

- Ya ce ya tsinkayi faduwar Jonathan a zaben kuma ya shawarce shi cewa hasashen da aka yi kan tsarin kada kuri'ar arewa ba daidai ba ne

Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya David Mark ya ce ya gargadi tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan kan irin makircin da 'yan arewacin kasar ke shiryawa domin kayar da shi a zaben 2015.

Mista Mark, wanda ya bayyana hakan a littafin ‘Against the Run of Play’, wanda fitaccen mai sharhin nan na jaridar ThisDay Olusegun Adeniyi ya wallafa, ya ce da gangan jam'iyyar PDP, a karkashin Ahmad Adamu Mu'azu ta gaya wa Mista Jonathan cewa zai lashe zaben bisa dogaro da hasashe kan tsarin kada kuri'ar da 'yan arewacin kasar za su yi.

A cewar Mark: "Na tsinkayi faɗuwar Jonathan a zaben kuma na nuna masa hakan, sannan na bayyana masa cewa hasashen da wasu mutane da ke kusa da shi suka yi kan tsarin kada kuri'ar da za a yi a arewa ba daidai ba ne."

Na gargaɗi Jonathan kan makircin 'yan Arewa – Inji David Mark

Goodluck Jonathan, mai dakinsa Patience da David Mark

"Na gane makircin da aka kitsa da kuma taron dangin da aka yi a arewa domin ganin Jonathan bai cimma burinsa ba, domin wadanda ke kusa da shi na ganin babu yadda shugaban kasa da ke kan mulki, kuma a jam'iyyar PDP ya fadi a zabe" , inji Mr Mark.

KU KARANTA KUMA: Babu inda yara ke karatun allo da bara kamar a arewacin Najeriya – Inji Sarkin Ningi

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, tsohon shugaban majalisar ta dattawan Najeriya ya ce wasu mutane sun rika yaudarar Mista Jonathan suna gaya masa cewa ba zai sha kaye a zabe ba kuma mataimakin shugaban kasar Namadi Sambo ya gane cewa yaudarar tsohon shugaban kasar ake yi "amma ban san irin tasirin da yake da shi a yakin neman zaben ba. Kuma har yanzu ina matukar mamakin yadda Jonathan ya kasa gane cewa ana yaudararsa har sai da lokaci ya kure".

Mista Mark ya ce Goodluck Jonathan da mai dakinsa Patience ne suka sa tsohon kakakin majalisar wakilan kasar Aminu Waziri Tambuwal ya bijire musu saboda wulakacin da suka rika yi masa.

A cewarsa, sun yi zaton shi da Tambuwal na son yin takarar shugabancin kasar a shekarar 2015, amma "na gaya wa Jonathan ni da shi cewa duk wadanda ke ba shi irin wadannan labaran karya suke yi."

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kali gaskiyan bayani kan rikicin tsakanin hausawa 'yan arewa da kuma yorubawa a Ile-Ife

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel