Babu inda yara ke karatun allo da bara kamar a arewacin Najeriya – Inji Sarkin Ningi

Babu inda yara ke karatun allo da bara kamar a arewacin Najeriya – Inji Sarkin Ningi

- Sarkin Ningi, Alh. Inusa Muhammad Dan Yaya ya amince da batutuwan da ake yi na rashin ci gaban arewacin Najeriya, cewar gaskiya ne

- Sarkin ya shawarci shugabanin arewacin da su zauna su duba matsalolin da suka addabi arewa

- Ya ce ana danganta arewa da talauci da jahilci da rashin cigaba da dai sauransu

Mai Martaba Sarkin Ningi, Alh. Inusa Muhammad Dan Yaya Yana mai cewa batutuwan da ake yi na rashin cigaban arewacin Najeriya, "lallai akwai rashin cigaban".

Ya kira manyan arewa da gwamnatocin arewa da malaman addini su zauna su duba matsalolin da suka addabi arewa. Saboda matsalolin ana danganta arewa da talauci da jahilci da rashin cigaba da dai sauran abubuwa marasa dadi.

Sarkin ya cigaba da cewa akwai alamura da suka samo asali daga al'ada da ake dangantasu da addini alhali kuwa babu ruwansu da addini. Irinsu hade da jahilci suka sa yanki arewa take baya.

Akan abubuwan da sarkin Kano ke fada ya ce tana da wuya a fahimceshi da wuri domin mutum ne mai ilimi da kwakwalwa sai an yi nazari a hankali a gane abun da yake nufi.

Misali sarki Inusa Muhammad Dan Yaya ya ce yadda ake tafiya karatun allo a arewa duk duniya babu inda ake yin haka. Ya kara da cewa sai a tarawa malami yara dari biyu ko fiye da haka kuma ba'a san malamin ba. Shi kuma sai ya kwashi yaran ya tafi dasu. Ya ce yaro dan shekara bakwai ko takwas a daukeshi, misali, daga Kontagora a kaishi karatu a Nguru babu abinci, babu sutura babu iyaye, malamin bai sanshi sosai ba sai dai yaron ya dinga bara a gari. Daga karshe karatun ma bai samu ba.

KU KARANTA KUMA: Gwamnoni 5 da su ka hana a tsige Sarki Muhammadu Sanusi II

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, sarki Inuwa ya ce Idan an samu irin wadannan yaran a ayyukan ta'adanci babu mamaki saboda wani yaron da zara an kaishi karatu ya rabu da iyayensa ke nan har abada.

Sarki yace "al'amarin ya shafi al'adunmu, ya shafi tarbiyarmu, kuma zancen almjiranci da karatun allo da yawan auratayya barkatai suna cikin abubuwan dake yiwa mutanen arewa dabaibayi". Ya ce domin haka bai kamata a gurbata al'adu da addini ba.

Ya ce 'ya'yan da ake haifa amana ne Allah ya bamu, domin a tarbiyar dasu, a yi masu duk abun da ya kamata. Ya ce : "ka dauki yaro ka jefar dashi can wajen mil dari ko dubu, ina amana a nan?"

Ya kira su sarakuna da malamai da shugabannin siyasa lallai su zauna su fahimci lamarin dake yiwa cigaban arewa tarnaki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sariki Sanusi ya shawarci shugabannin Najeriya da shugabanci na nagari a cikin wannan bidiyo

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel