Za kayi mamaki idan kaji wanda yayi kokarin kashe Dino Melaye

Za kayi mamaki idan kaji wanda yayi kokarin kashe Dino Melaye

– Kwanaki muka samun labarin cewa an yi yunkurin hallaka Sanata Dino Melaye

– Melaye yace an kama wasu cikin masu nema su ga bayan sa

– Ciki har da hannun wani shugaban karamar Hukuma

Kuna da labari kwanaki Sanata Dino Melaye mai wakiltar Jihar Kogi ya sha da kyar.

Sanatan ya bayyana cewa an yi kokarin ganin bayan rayuwar sa.

Jami’an tsaro sun gano masu hannu cikin lamarin.

Za kayi mamaki idan kaji wanda yayi kokarin kashe Dino Melaye

Saura kiris a aika Sanata Melaye lahira

Sanata Dino Melaye mai wakiltar Yammacin Kogi yayi da’awar cewa wasu sun kai masa hari a gidan sa da ke Unguwar Ayetoro-Gbede da ke karamar Hukumar Ijumu na Jihar Kogi kwanakin baya.

KU KARANTA: Sarkin Ningi ya caccaki 'Yan Arewa

Wanda wannan ya jawo ‘yan magana tsakanin sa da abokan gaban siyasar ciki har da Gwamnan Jihar Yahaya Bello. Inda Melaye yake cewa Gwamnan ne ke kokarin ganin bayan sa don dama ba su ga maciji.

Yanzu dai mai magana da bakin ‘Yan Sanda Jimoh Mashood kamar yadda ku ka samu labari daga NAIJ.com ya gurfanar da wadanda ake zargi. Abin mamaki dai wani Taofiq Isah ne ya shirya wannan mummunan abu ta hannun wani wai shi Abdulmumuni Iron.

KU KARANTA: Sojin sama sun rusa 'Yan Boko Haram

Za kayi mamaki idan kaji wanda yayi kokarin kashe Dino Melaye

Wadanda su kayi kokarin kashe Dino Melaye

A wancan lokaci Sanata Melaye yace an dauki dogon lokaci ana luguden wuta a gidan cikin tsakiyar dare har yi masa asarar motoci. Rundunar ‘Yan Sanda lallai ta tabbatar da wannan ta kuma shirya bincike.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ya za ka yi da rayuwar ka [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel