Shugaba Buhari nada isashen lafiyar takara karo na biyu – Inji Amaechi

Shugaba Buhari nada isashen lafiyar takara karo na biyu – Inji Amaechi

- Ministan harkokin sufuri ya jaddada cewa shugaba Buhari nada isashen lafiyar takara karo na biyu a zabe mai zuwa a 2019

- Amaechi ya kara da cewa zai ba shugaba Buhari goyon baya dari bisa dari idan ya fito zai yi takara a zaben 2019

Ministan harkokin sufuri kuma tsohon gwamnan Jihar Ribas, daya daga cikin jihohin masu arzikin man fetur a yankin Neja Delta, Rotimi Amaechi, ya yi imani shugaba kasa Muhammadu Buhari nada isashen lafiyar takara karo na biyu a 2019.

Ministan ya yi wannan bayyana ne ganin an dauki lokaci ana kace-nace game da batun lafiyar shugaban tarrayar Najeriya da ke kara nuna alamu na kauracewa bainar jama'a. Daga dukkan alamu rudanin yana shirin kara karuwa bayan share tsawon wannan mako ba tare da ganin shugaban a cikin jama'a ba.

NAIJ.com ta ruwaito cewa, shugaba Buhari ya kauracewa halartar taron majalisar kasar na mako-mako cikin tsakiyar wannan mako dai, bangaren gwamnatin na kafa hujja ne da zabi na shugaban na yin aiki ko dai daga kuryar daki ko kuma a cikin ofishin da gwamnatin kasar ta gina domin aikin nasa.

Shugaba Buhari nada isashen lafiyar takara karo na biyu – Inji Amaechi

Shugaba Buhari na gaisawa da Rotimi Amaechi

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari na bukatar addu'a - Sako daga fadar shugaban kasa

A lokacin da aka tambaye ministan cewa zai iya goyi bayan shugaba Buhari idan ya sake tsayawa zabe a 2019, Amaechi ya ce: "Zan ba shi goyon bayana dari bisa dari”.

Shugaba Buhari dai ya yi bayyanarsa ta karshe a bainar jama'a ne a ranar Juma'ar makon jiya a massalacin fadar gwamnatin kasar ta Aso Rock

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kali bidiyon da ministan sufuri Rotimi Amaechi ya ce yana kan hanya yana aiki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel