Babachir Lawal ya shiga uku ya lalace

Babachir Lawal ya shiga uku ya lalace

– Shugaban kasa Buhari ya dakatar da Sakataren Gwamnatin sa

– An bada umarni ayi bincike kana a hukunta mara gaskiya

– Ana zargin Babachir da bada kwangila ba tare da ka’ida ba

Kamar yadda ana nan ana binciken shugaban Hukumar NIA na kasa.

Mataimakin shugaban kasa na kuma binciken Sakataren Gwamnatin Tarayya Mr. Babachir David Lawal.

Kuma da alamu Babachir ba zai ji da dadi ba.

Babachir Lawal ya shiga uku ya lalace

Babachir David Lawal tare da shugaban kasa a taro

Fadar shugaban kasa ta dakatar da Sakataren Gwamnatin Tarayya Injiniya Babachir David Lawal tare da shugaban Hukumar NIA mai leken asiri bisa wasu zargi dabam-daban. Tuni aka nada kwamiti domin binciken su wanda har an yi nisa.

KU KARANTA: Shugaban kasa ya tuna da Fulani

Babachir Lawal ya shiga uku ya lalace

Lokacin da Babachir Lawal ya bar ofis

Yanzu haka NAIJ.com na ji cewa Babachir din fa ba zai ji da dadi ba ganin yadda abubuwa su ke tafiya. Kwamitin da aka nada karkashin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo tace babu wani daga kafa da za tayi.

Zuwa Laraba dai za a kammala binciken inda mu ke jin cewa ma dai tuni har an fara aika wadanda aka samu da laifi zuwa Hukumar EFCC ta kasa. A makon jiya an dauki dogon lokacin ana jefawa su Babachir din tambayoyi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Nnamdi Kanu ya bar gidan yari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu
NAIJ.com
Mailfire view pixel