Ba mamaki darajar Dala ta fadi kasa

Ba mamaki darajar Dala ta fadi kasa

– Darajar Dala na iya faduwa kasa kwanan nan

– CBN na daukar wani mataki na musamman

– Hakan zai sa a samu Dala a gari

Shekaran jiya mun samu cewa Naira ta tashi a kasuwar canji.

Babban bankin kasar CBN na cigaba da sakin daloli a kasar.

Hakan na iya sa Dalar ta rage farashi.

Ba mamaki darajar Dala ta fadi kasa

CBN na kokari wajen tada Naira

Makon jiya ne NAIJ.com ta rahoto cewa CBN ta saki Dala Miliyan 246 a Ranar Litinin. Sakin kudin da CBN ke yi ne ya kai har Dalar ta dan fadi a kasuwa. Gwamnan Babban bankin kasar Godwin Emifiele ya bayyana cewa Najeriya na daf da fita daga cikin matsin tattali.

KU KARANTA: Dangote ya ci riba a shekarar bara

Yanzu haka babban bankin kasar ya kara sakin wasu Dala 20, 000 ga kowane dan canji watau Bureau De Change da ke da rajitsa. Wannan zai matukar taimakawa wajen samun isassun Daloli na zagaye a hannun Jama’a masu bukata.

CBN din na saida Dalar ne a kan N360 ga ‘Yan kasuwa wanda su kuma kan saida kan N380 musammam a Birnin Abuja da Garin Legas. Bankin kuma ya ware wasu Dala Miliyan 100 domin masu saye kan sari.

KU KARANTA: Manoman Arewa na ta keta hazo ba kaukautawa

Ba mamaki darajar Dala ta fadi kasa

Gwamnan babban banki CBN

Kwanakin baya Shugaban Yan canji Aminu Gwadabe ya yabawa bankin CBN wajen sakin makudan miliyoyi a kasuwa. Gwadabe yace hakan zai yawaita Dalar Amurka a kasar ya kuma hana badakalar da ke cikin kasuwar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ka ji yadda wata mata ta ran sa dan ta

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel