Amurka zata tallafawa arewa maso gabashin Najeriya a dalla miliyan 30

Amurka zata tallafawa arewa maso gabashin Najeriya a dalla miliyan 30

- Kasar Amurka ta yi alkawarin tallafawa gwamnatin Najeriya da dalla miliyan 30

- Amurka ce ke kan gaba wajen samarda tallafin jinkai a kasashen yankin tafkin Chadi

- Wannan tallafin zai marawa shirin majalisar dinkin duniya na samarda tallafin nau’oin abinci daban daban a yankin

Amurka ta bada sanarwa karin tallafin dala miliyan talatin domin tallafawa al’umar yankin arewa maso gabashin Najeriya inda aika aikar tsagerun ‘yan Boko Haram ya haddasa matsaloloin jinkai da dama.

Wannan Karin taimako zai marawa shirin majalisar dinkin duniya na samarda tallafin nau’oin abinci daban daban da kuma agajin kudaden siyan abincin a yankunan da yanzu ake hada hadar kasuwanci.

Za kuma ayi amfani da wani bangare na kudaden wajen tallafawa komawa aikin gona ga al’umomin da zaman lafiya ya dore a yankunansu a halin yanzu.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labara, tun daga watan Oktoba na shekarar 2015, Amurka ce ke kan gaba wajen samarda tallafin jinkai a kasashen yankin tafkin Chadi inda ta bada taimakon zunzurutun kudi har dala miliyan 452 ga jama’ar da wannan ja’ibar wannan tarzomar ta Boko Haram, ta rutsa dasu.

KU KARANTA KUMA: Ba mamaki darajar Dala ta fadi kasa

Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar, ta nuna cewa Amurkan zata ci gaba da yin aiki tare da gwamnatin tarayyar Najeriya da sauran kungiyoyin jinkai domin samarda taimako a kaucewa ja’ibar yunwa sannan a marawa al’umomin dake cikin mawuyacin hali.

A bayan dai majalisar dinkin duniya, ta yi gargadin cewa muddin bai ayi wani abu cikin gaggawa ba toh yunwa ka iya tagayyara miliyoyin mutane kuma tana iya kasancewar miliyoyin kananan yara su rasa rayuwarsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yaya za ka ji idan shugaban kasar Amurka Donald trump ya ce zai bamai Boko Haram kamar

Siriya?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel