An damke wadanda sukayi yunkurin kashe Sanata Dino Melaye

An damke wadanda sukayi yunkurin kashe Sanata Dino Melaye

- An damke mutane 6 game da kisan sanata Dino Melaye

- Daga cikin wadanda aka kama wani shugaban karamar hukuma ne da kuma dan sanda

Bisa ga yunkurin kisan Sanata Dino Melaye kwanakin baya, hukumar yan sanda Najeriya ta damke mutane 6 a yanzu.

NAIJ.com ta samu rahoton cewa daga cikin wadanda aka kama shine shugaban karamar hukumar Ijimu ta jihar Kogi, Taofiq Isah.

Sunayen wadanda aka kama shine Taofiq Isah, 54, James Ede, 36, Ade Obage, 29, Abdullahi Isah,32, Ahmed Ajayi, 45, da Michael Bamidele, 26.

Kakakin hukumar yan sandan tarayya, Jimoh Moshood, wanda yayi magana da manema labarai yaci an kwace wata motar asibiti, bindigar AK47 guda 5, bindigar gargajiya 2, carbin harsasai 25 da sauran su.

An damke wadanda sukayi yunkurin kashe Sanata Dino Melaye

An damke wadanda sukayi yunkurin kashe Sanata Dino Melaye

Moshood yace: “ An aika makaman dakin gwaji domin gwada su a ofishin ilimi da leken asirin hukumar da ke Legas.”

Moshood ya kara da cewa daya daga cikin wadanda suka kai harin Obage ne ya kaow kara ofishin yan sanda . amma har da shi aka kama kuma ana gudanar da binciken rawan da ya taka a harin.

KU KARANTA: An sake Nnamdi Kanu

Yace: “Obage ne ya zo ya bayyanawa yan sanda cewa yanada masaniya game da wadanda suka sukayi kokarin kashe Sanata Dino Melaye bayan sun kai harin.

''Kana ya sanar da yan sanda cewa shugaban makasan , Abdullahi Eko ne ya gayyacesa kuma shima yana hannu.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

An saki shugaban kungiyar Biyafara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel