Mutan Arewa sun fara maganganu game da rashin lafiyan Baba Buhari, musamman Katsinawa

Mutan Arewa sun fara maganganu game da rashin lafiyan Baba Buhari, musamman Katsinawa

-Mutanen jihar Katsina sun bayyana ra’ ayoyinsu game da rashin lafiyan shugaba Buhari

-Kowa dai na nuna tsoronsa idan Allah ya kaddara abinda ba’a so ya faru

Ko shakka babu rashin lafiyan shugaban Muhammadu Buhari na tayar da hankalin mutane musamman yan jiharsa ta Katsina.

Abdulrasheed Funtua, malami a wata jami’a a Katsina yayi kira ga mutane su taimakawa shugaban kasa da addu’ a.

Yace: “ Rashin lafiyan shugaba Muhamadu Buhari kaddara ne kuma rashin lafiya ba mutuwa bane. Ka dauki misali da mutuwan sanata Adeleke, bai yi rashin lafiya ba amma ya mutu. Saboda haka kaddara ne kuma babu abinda amu iya yi face addu’ a ga shugaba Buhari."

Mutan Arewa sun fara maganganu game da rashin lafiyan Baba Buhari, musamman Katsinawa

Mutan Arewa sun fara maganganu game da rashin lafiyan Baba Buhari, musamman Katsinawa

Wani mazaunin Kankia, Ustaz Idris, yace akwai tsoro tattare da rashin lafiyan shugaban kasa saboda irin wahalan da muka sha bayan mutuwan shugaba Yar’ adua da Jonathan ya hau mulki.

Yace: “ Kawai addu’an da mukeyi shuine shugaba Buhari ya samu lafiya kuma ya karasa mulkinsa mai kyau kamar yadda ya fara.” Idris yace.

Shugaban wata kungiyar fafutuka wato Accountability and Good Governance Initiative, Lawal Saidu Funtua, shima ya bayyana irin wannan ra’ayin musamman bayan jihr Katsina tayi rashin Umaru Musa Yardaua a irin wannan hali.

KU KARANTA: Abdulmumini Jibrin ya dira kotu da lauyoyi 30

Yayi addu’a ubangiji ya baiwa shugaban kasa lafiya ya karashe ayyukan da ya fara yi musamman na yaki da rashawa saboda kada a fuskanci ci baya.

Shi kuma a bangaren sa, shugaban jam’ iyyar National Conscience Party, NCP,shiyar jihar Katsina, Shehu Sani yace kawai shugaba Buhari yayi murabus.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An mutu da yawa a wani karanbatta da aka sha tsakanin Yansanda da masu haƙe-haƙen ma’adanai

An mutu da yawa a wani karanbatta da aka sha tsakanin Yansanda da masu haƙe-haƙen ma’adanai

An mutu da yawa a wani karanbatta da aka sha tsakanin Yansanda da masu haƙe-haƙen ma’adanai
NAIJ.com
Mailfire view pixel