Madallah! Albishirin ku fulanin Najeriya, sako daga Gwamnatin Buhari (Karanta)

Madallah! Albishirin ku fulanin Najeriya, sako daga Gwamnatin Buhari (Karanta)

- Hukumar ilmantar da yayan Fulani makiyaya ta kasa ta kaddamar da shirin ziyarar gani da ido makarantun yayan Fulani makiyaya a shiyyar arewa maso yamma.

- Daraktan wayar da kan jama’a na hukumar Alhaji Muhammad Dan-Iya Faty ya sanar da hakan jim kadan da rangadin wasu makarantun yayan Fulani makiyaya.

Yace shi da jami’an hukumar 29 an turo su jihar Jigawa domin gudanar da shirin na kwanaki 12.

Alhaji Muhammad Dan-Iya Faty yace makasudin shirin shine ganin halin da makarantun suke ciki akwai da kuma irin cigaban da ilmin yayan Fulani makiyaya ya samu da kuma akasin hakan.

NAIJ.com ta tattaro cewar yace ana gudanar da shirin ne a makarantun yayan Fulani makiyaya 281 dake shiyoyin Dutse da Birnin Kudu da Kafin Hausa da Hadejia da Kirkasamma da Kazaure da Gumel da kuma Ringim.

Madallah! Albishirin ku fulanin Najeriya, sako daga Gwamnatin Buhari (Karanta)

Madallah! Albishirin ku fulanin Najeriya, sako daga Gwamnatin Buhari (Karanta)

KU KARANTA: Patience Jonathan ce ta kada mijin ta zabe

Daraktan ya kara da cewar shirin zai shafi dalibai dubu hudu da suka kammala karatu a makarantun yayan Fulani makiyaya na sassan jihar.

Yace bankin raya kasashen afirka ya tallafawa hukumar da cibiyoyin koyan sanaoi biyu dake Kachia a jihar Kaduna da kuma ta Abuja domin amfanin makiyaya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel