Shugaba Buhari ya shiga tsakanin rikicin ‘Yan Sanda da Majalisa

Shugaba Buhari ya shiga tsakanin rikicin ‘Yan Sanda da Majalisa

– Shugaba Buhari ne ya shiga tsakanin Sanata Goje da ‘Yan Sanda

– Har yau Majalisa ba ta tabbatar da kasafin kudin bana ba

– Sanata Danjuma Goje yace ‘Yan Sanda sun yi gaba da takardun a gidan sa

Kuna da labari cewa kwanaki Shugaban kwamitin kasafin na Majalisar Dattawa Sanata Danjuma Goje yace ‘Yan Sanda sun yi awon gaba da takardun kasafin kudi..

Wannan ya faru ne a makon baya da suka kai wani samame gidan sa.

Shugaba Buhari ya shiga tsakanin rikicin ‘Yan Sanda da Majalisa

Sanata Goje na Majalisar Dattawa

Wannan ya sa ba a kammala aikin kasafin kudin ba kamar yadda Majalisar ta bayyana. Sai dai Sanata Ita Enang ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga tsakanin Sufetan ‘Yan Sandan kasar da Sanatan.

KU KARANTA: A binciki Goje inji Shekarau

Shugaba Buhari

Shugaba Buhari tare da Sakataren Gwamnatin da aka dakatar

Enang yake cewa bayan shugaban kasar ya sa baki aka maidawa Sanatan duk abubuwan da aka karba daga gidan na sa. Da farko dai ‘Yan Sanda sun ce sam ba su dauki takardun kasafin kudin kasar daga gidan sa ba sai dai wasu makudan kudi.

‘Yan Sanda dai sun bada hakuri game da samamen da su ka kai wanda ya kawo tasgaro wajen aiki kan kasafin kudin kasar. Sanata Ahmed Lawan ya tabbatar da cewa suna kokarin ganin an kammala aikin da ya rage zuwa mako mai zuwa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda aka rasa wani barden Soji

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sanata Shehu Sani ya lissafa wasu muhimman matakai daya zama wajibi a ɗauka don sake raya Arewa

Sanata Shehu Sani ya lissafa wasu muhimman matakai daya zama wajibi a ɗauka don sake raya Arewa

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel