Kwamitin Osinbajo ta ma gwamnan CBN tambayoyi akan kudin Ikoyi

Kwamitin Osinbajo ta ma gwamnan CBN tambayoyi akan kudin Ikoyi

- Shugaban babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya gurfana domin bincike

- Kwamitin Osinbajo na gudanar da binciken sakataren da aka dakatar da kuma shugaban NIA, Femi Oke

- Ana sa ran kwamitin zata kammala aikinta ba da dadewa ba

Shugaban babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ne na gaba wanda ya bayyana gaban kwamiti mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo.

Ana gayyaci Emefiele ne bisa ga maganar diraktan NIA da aka dakatar , Ayo Oke.

An dakatad da Babachir David Lawal ne bisa gas aba dokan Najeriya wajen bayar da kwangila a shirin fadar shugaban kasa domin taimakawa yankin arewa maso gabas.

Kwamitin Osinbajo ta ma gwamnan CBN tambayoyi akan kudin Ikoyi

Kwamitin Osinbajo ta ma gwamnan CBN tambayoyi akan kudin Ikoyi

Wata kwamiti karkashin Sanata Shehu Sani ta bankado cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayyan ya bayar da N220m domin yanke ciyawa a sansanin yan gudun hijra da ke Yobe.

Shi kuma shugaban NIA, Ayo Oke, an dakatad da shi ne bisa ga kudi $43.4million da aka gano a wata daki da ke unguwar Ikoyi bayan yace ain a hukumar ne.

KU KARANTA: Kayar Ingila tayi raddi ga Jonathan

NAIJ.com ta tattaro cewa Emefiele ya bayyana a gaban kwamitin ne tare da wasu yan kwangilan da aka ba aiki a shirin fadar shugaban kasan akan arewa maso gabas.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel