Rashin cigaban Arewa: Atiku ya bayyana laifin su waye

Rashin cigaban Arewa: Atiku ya bayyana laifin su waye

– Atiku Abubakar ya ba mutanen Arewa shawara

– Tsohon mataimakin shugaban kasar yace mu muka kashe Arewar

– Turakin Adamawa ya bayyana wannan ne a Abuja

Turakin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar yayi kira ga mutanen Arewa.

Atiku yace a daina zargin kowa wajen rashin cigaban da Yankin ya samu.

Yake yake cewa babu laifin kowa illa mu mutanen da kan mu ba wani ba.

Rashin cigaban Arewa: Atiku ya bayyana laifin su waye

Atiku ya bayyana inda matsalar ta ke

Tsohon shugaban kasar yayi wannan kira ne a wani dakin taro na Sojojin saman Najeriya inda yace ‘Yan Arewa su daina ganin kowa da laifi wajen koma-bayan da Yankin ya samu da rashin cigaba.

KU KARANTA: Ina bayan Bukola Saraki-Sarkin Ningi

Rashin cigaban Arewa: Atiku ya bayyana laifin su waye

Turakin Adamawa Atiku Abubakar

Atiku Abubakar yake cewa idan har Jama’a su ka rika daurawa wasu laifi ba abin da za su ci ma face bakin ciki. Duk da cewa Atiku na ganin Arewa ce koma-baya a Kasar yace bai yarda a raba Najeriya ba. Sai dai fa akwai karin barazana na rashin hadin-kai a kasar.

Kwararren Ma’aikacin bankin nan Alhaji Falalu Bello ya bayyana cewa Kudancin kasar nan sun yi wa Arewa nisa duk da cewa da ana tafiya kafada-kafada. Yanzu an yi Arewacin kasar wani finitinkau sai dai yace Arewa ba Matsiyata bane.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Tafiyar shugaba Buhari Landan

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
NAIJ.com
Mailfire view pixel