Gwamnatin Birtaniya ta mayar da martani ga Goodluck Jonathan

Gwamnatin Birtaniya ta mayar da martani ga Goodluck Jonathan

-Gwamnatin Ingila tayi raddi ga Ebele Jonathan akan baranbaraman da yayi

-Tace kawai yan Najeriya sun zabi wanda suke so ne

Gwamnatin kasar Birtaniya ta yi raddi ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan akan zargin da yayi mata cewa ta munafinceshi a zaben da ya sha kasa a shekarar 2015.

Jonathan ya bayyana wannan ne a wata littafi mai suna “Against the Run of Play,” shugaban majalisan jaridar Thisday, Olusegun Adeniyi, ya rubuta.

Yayinda take mayar da martani, ofishin jakadan Birtaniya da ke Najeriya ta saki wata jawabi ranan Juma’a inda tace zaben 2015, ra’ayin yan Najeriya ne.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta bayyana yawan kudin da ta gano

Kasar Ingila tace rawan da ta taka kawai shine hada kai da yan Najeriya da shugabanninsu wajen tabbatar da cewa anyi zabe cikin zaman lafiya da lumana.

Kafin zaben 2015, kasar Ingila ta hada kai da yan Najeriya da shugabanninsu wajen tabbatar da cewa anyi zabe cikin zaman lafiya da lumana da kuma baiwa kowa daman zaban wanda ranshi ya so.

“Mun yabawa shugaban Jonathan akan sauka daga ragamar mulki da yayi a 2015 cikin lumana bayan ya sha kasa.”

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel