Bayan Sarki Sanusi, Sanrkin Ningi ma ya caccaki Arewa (Karanta)

Bayan Sarki Sanusi, Sanrkin Ningi ma ya caccaki Arewa (Karanta)

- Majiyar mu ta zanta da Sarkin Ningi Mai Martaba Inusa Muhammad Dan Yaya wanda yace yayi magana ne a matsayin dan kasa dake da 'yancin yayi magana akan wasu abubuwa.

- Yana mai cewa batutuwan da ake yi na rashin cigaban Arewacin Najeriya, "lallai akwai rashin cigaban".

Ya kira manyan arewa da gwamnatocin arewa da malaman addini su zauna su duba matsalolin da suka addabi arewa. Saboda matsalolin ana danganta arewa da talauci da jahilci da rashin cigaba da dai sauran abubuwa marasa dadi.

NAIJ.com ta tsinkayi Sarkin ya cigaba da cewa akwai alamura da suka samo asali daga al'ada da ake dangantasu da addini alhali kuwa babu ruwansu da addini. Irinsu hade da jahilci suka sa arewa take baya.

Akan abubuwan da Sarkin Kano ke fada yace tana da wuya a fahimceshi da wuri domin mutum ne mai ilimi da kwakwalwa sai an yi nazari a hankali a gane abun da yake nufi.

Misali Sarki Inusa Muhammad Dan Yaya yace yadda ake tafiya karatun allo a arewa duk duniya babu inda ake yin haka. Yace sai a tarawa malami yara dari biyu ko fiye da haka kuma ba'a san malamin ba. Shi kuma sai ya kwashi yaran ya tafi dasu. Yace yaro dan shekara bakwai ko takwas a daukeshi, misali, daga Kontagora a kaishi karatu a Nguru babu abinci, babu sutura babu iyaye, malamin bai sanshi sosai ba sai dai yaron ya dinga bara a gari. Daga karshe karatun ma bai samu ba.

Idan an samu irin wadannan yaran a ayyukan ta'adanci babu mamaki saboda wani yaron da zara an kaishi karatu ya rabu da iyayensa ke nan har abada.

Bayan Sarki Sanusi, Sanrkin Ningi ma ya caccaki Arewa (Karanta)

Bayan Sarki Sanusi, Sanrkin Ningi ma ya caccaki Arewa (Karanta)

KU KARANTA: Sojin Najeriya sunyi raga-raga da yan Boko Haram

Mai Martaba yace batun nan da ake yi Sa'adu Zungur ya yita cikin wakarsa a shekarar 1947. Yace matukar arewa yara suna bara a birni da kauyuka suna cewa "Allah Ya baku, mu samu abun miya" yace babu shakka sai arewa ta sha wuya. Yace kome arewa ke dashi idan ba ilimin na sarafar dashi talauci ba zai bar arewa ba.

Sarki yace "al'amarin ya shafi al'adunmu, ya shafi tarbiyarmu, kuma zancen almjiranci da karatun allo da yawan auratayya barkatai suna cikin abubuwan dake yiwa mutanen arewa dabaibayi". Yace domin haka bai kamata a gurbata al'adu da addini ba.

Yace 'ya'yan da ake haifa amana ne Allah ya bamu, domin a tarbiyar dasu, a yi masu duk abun da ya kamata. Yace "ka dauki yaro ka jefar dashi can wajen mil dari ko dubu, ina amana a nan?"

Ya kira su sarakuna da malamai da shugabannin siyasa lallai su zauna su fahimci lamarin dake yiwa cigaban arewa tarnaki.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel