Fadar Shugaban Kasa ta yi bayani a kan badakalar daukar SSS

Fadar Shugaban Kasa ta yi bayani a kan badakalar daukar SSS

Fadar Shugaban kasa ta nisanta kanta da rahoton da ake cewa hukumar tsaro ta SSS ta fifita jihar Katsina da Shugaban Kasa ya fito da Shugaban hukumar Lawal Daura.

Fadar shugaban kasar ta bayyana cewa kason da jaridu suka buga na fifikon Katsina da Arewa ba gaskiya bane.

Sai kuma ta bayyana cewa anyi hakan ne domin a gyara bannar da akayi a shekarun baya musamman wajen ganin mafi yawan wadanda ke aiki a ma'aikatar ba yan arewa bane.

A jiya ne dai Wata harkallar da aka bankado ta dabaibaye hukumar ‘yan sandan leken asiri na farin kaya, SSS, inda aka gano son kai da nuna bangaranci wajen daukar ma’aikatan da aka yi a hukumar, wadanda suka kammalla karbar hoto kwanan baya a jihar Legas.

Fadar Shugaban Kasa ta yi bayani a kan badakalar daukar SSS

Fadar Shugaban Kasa ta yi bayani a kan badakalar daukar SSS

KU KARANTA: Buhari ya hakura da mulki ya ba Osinbajo - Makarfi

NAIJ.com ta samu labarin cewa hukumar dai ta kaddamar da jami’ai 479 da ta dauka, wadanda ta yaye a Legas ranar 5 ga Maris, 2017. An yaye su ne bayan sun samu horo a fannin dakile harin sari-ka-noke, leken asiri, binciko bayanai, koyon sarrafa bindigogi da horo na motsa jiki.

Sunayen jami’an tsaron wanda Premium Times ta samu, ya nuna irin yadda ba a yi raba-daidai ba tsakanin jihohin kasar nan 36 da Babban Birnin Tarayya, a wajen daukar ma’aikatan.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan ma dai wasu ne da suka zo suna cewa an kama mazajen su

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel