Patience Jonathan ce ta sabbaba fadin mijinta a zaben 2015 - David Mark

Patience Jonathan ce ta sabbaba fadin mijinta a zaben 2015 - David Mark

-David Mark ya bayyana gulmace-gulmacen da Mrs Patience Jonathan keyi

-Yace irin wannan abu ne ya sanya aka juyawa Jonathan baya a zabe

Tsohon shugaban majalisan dattawa, David Mark, ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya rasa manyan yan jam’iyyar PDP wadanda suka yaudaresa a zabe saboda zarge-zargen matarsa, Patience Jonathan.

Tsohon shugaban majalisan dattawan ya bayyana cewa Jonathan da matarsa sun zamar da tsohon kakakin majalisan wakilai, Tambuwal, dan adawa.

Alakar da ke tsakanin Tambuwal da Jonathan ba mai kyau bace, wanda ya sabbasa ya sheke jam’iyyar APC daga baya.

KU KARANTA: Hukumar Soji tayi rugu-rugu da mabuyar Boko Haram

David Mark yace yayi iyakan kokarinsa wajen gyara barakar da ke tsakanin Tambuwal da Jonathan amma basu gushe suna kallon Tambuwal a matsayin dan adawa ba.

Mark yace : “ Na kai shi (Tambuwal) da Emeke zuwa wajen shugaban kasa inda suka tabbatar da cewa zasu mara ma wannan gwamnati baya. Amma ba’a gushe ana samun matsala daga wajen Jonathan ba cewa Tambuwal mai son girma ne.

“Na san (Patien) na zargi na amma bata iya fada min ido da ido ba. Ta taba cewa Sanata Joy Emordi cewa ‘ Joy, naji ance kai ne manajan kamfen David Mark na takarar shugaban kasa,’ kuma wannan karya ne.

“Sai da na gana da shugaban kasa domin sulhunta wannan abu.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel