Hukumar sojin saman Najeriya ta ragargaza atilarin yan Boko Haram a Sambisa

Hukumar sojin saman Najeriya ta ragargaza atilarin yan Boko Haram a Sambisa

-Hukumar NAF ta kai hari wata mabuyar Boko Haram a Sambisa

-Ta kai harin ne da jiragen saman yaki inda musu ruwan wuta

Hukumar sojin saman Najeriya a ranan Juma’a ta samu nasarar ragargaza atilarin yan Boko Haram a dajin Sambisa.

Kakakin hukumar sojin saman, Air Commodore Olatokunbo Adesanya, ya bayyana wannan ne a wata jawabi ranan Juma’a a Abuja.

Adesanya yace an boye atilarin ne karkashin wata bishiya inda jami’an leken asirin hukumar ta gano yayinda take fatrol a yankin.

Hukumar sojin saman Najeriya ta ragargaza atilarin yan Boko Haram a Sambisa

Hukumar sojin saman Najeriya ta ragargaza atilarin yan Boko Haram a Sambisa

Yace : “Jami’ an leken asiri sukayi kira na gaggawa domin kai hari wurin. Saboda haka, jirgin Alpha Jet da F-7Ni sun kai farmaki wurin."

KU KARANTA: An saki shugaban kungiyar IPOB Nnamdi Kanu

“Bayan jiragen guda biyu sun far ma wurin, sai da kawai ya kama da wuta.

“Baya haka, an bayyana bidiyon yadda jiragen sukayi rugu-rugu da atilarin.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Mata masu juna 100 suka rasa rayukan su a jihar Zamfara - Ma'aikacin asibitin Gusau

Mata masu juna 100 suka rasa rayukan su a jihar Zamfara - Ma'aikacin asibitin Gusau

Mata masu juna 100 suka rasa rayukan su a jihar Zamfara - Ma'aikacin asibitin Gusau
NAIJ.com
Mailfire view pixel