Hukumar EFCC ta gano N17bn sakamakon sabon shirin cinne– Ibrahim Magu

Hukumar EFCC ta gano N17bn sakamakon sabon shirin cinne– Ibrahim Magu

- Ibrahim Magu ya bayyana yawan kudin da hukumar EFCC ta gano

- Yace suna zage damtse wajen yakan rashawa kafin ta hallaka Najeriya

- Shugaban NUJ ya nuna goyon bayansu ga hukumar EFCC

Mukaddashin shugaban hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, Ibrahim Magu, a ranan Alhamis 27 ga watan Afrilu 2017 ya bayyana cewa shirin tonan asirin da gwamnatin tarayya ta samarya taimaka wajen bankado kudi N17billion.

Magu ya bayyana wannan ne yayinda yake gabatar da wata takarda mai take ‘Kafin rashawa ta kashe Najeriya’, a taron bada lambar yabon gamayyar yan jaridan Najeriya, da akayi a Ladi Kwali Hall, Sheraton Hotels, Abuja.

A jawabin, wanda Dakta A. Bello ya wakilcesa yace, “ banda wasu abubuwan da aka gano sanadiyar shirin tonan asiri, hukumar EFCC ta gano kudade N521,815,000, $53,272,747, £122,890, da €547,730.”

Hukumar EFCC ta gano N17bn sakamakon sabon shirin cinne– Ibrahim Magu

Ibrahim Magu

''Hukumar EFCC ta dukufa da ganin cewa ta ceto Najeriya da mutanenta kafin rashawa ta kashe ta. Muna kira gay an jarida da yan Najeriya na kwarai su bamu goyon baya wajen wannan yaki. Da kokarin gwamnatin Najeriya d akuma mutane, hukumar EFCC zata samu nasara.”

Magu yace sunyi kamu 62 cikin watanni 3 na fari wannan shekara.

KU KARANTA: Makarfi yace Buhari ya hakura kawai ya sauka daga mulki

A jawabinsa, shugaban gamayyar yan jarida, Abdulwaheed Odusile, yayi alkawarin goyon bayan kungiyar ga EFCC kuma ya yabawa hukumar akan kokarin da takeyi wajen yaki da rashawa.

Yayi kira ga hukumar ta cigaba da aikinta ba tare da tsoron kowa ba ko kuma son kai. Kana kuma ya soki majalisan dattawa akan rashin tabbatar da Magu a matsayin shugaban hukumar.

https://web.facebook.com/pg/naijcomhausa/posts/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon shugaban kungiyar IPOB bayan an saki shi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel