Shugaba Buhari ya mika ragamar mulki ga Osinbajo – Sanata Makarfi

Shugaba Buhari ya mika ragamar mulki ga Osinbajo – Sanata Makarfi

-Shugaban kwamitin rikon kwaryan jam’iyyar PDP yace Buhari ya sauka daga karagar mulki

-Yace ya je ya huta har sai ya samu cikakken lafiya

Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP, Senator Ahmed Makarfi, yayi kira ga shugaba Muhammdu Buhari da ya mika ragamar mulki ga mataimkainsa Yemi Osinbajo.

Makarfi yace Buhari bai da lafiyan cigaba da zama a ofishi, da zai fi idan shugaban ya mika ragamar mulki ga Osinbajo kafin ya samu cikakken lafiya.

Yace: “ Wannan ba daidai bane kuma bai kamata ba. ra’ ayina shine shugaban kasan bai da karfin zama a ofis, da yafi kawai ya bayyanawa yan Najeriya saboda mataimakinsa ya cigaba a matsayin mukaddashin shugaban kasa.

Shugaba Buhari ya mika ragamar mulki ga Osinbajo – Sanata Makarfi

Shugaba Buhari ya mika ragamar mulki ga Osinbajo – Sanata Makarfi

“Wannna ba zancen ko dan APC bane ke rashin lafiya. Addu’ a na shine ya samu lafiya ya karashe mulkinsa.”

“A matsayina na dan siyasa, ina son ya kareshe mulkinsa. Idan mutane suka fara yada jita-jitan su, sun sani cewa babu wani amfani ga PDP idan Buhari bai sami daman karasa mulkinsa ba.”

KU KARANTA: Nnamdi Kanu ya cika sharrudan beli

“Muna son ya samu lafiya, muna son ya cigaba da mulki har 2019 saboda idan muka shiga zabe zamu kayar da APC”

“Bamu son wani rikicin siyasa a kasan nan.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel