Majalisar wakilai ta yi tir da harin kisa a kan Dino Melaye

Majalisar wakilai ta yi tir da harin kisa a kan Dino Melaye

- Majalisar wakilai ta yi kira ga sufeto-Janar na ‘yan sanda da ya gurfanar da wadanda ke bayan harin kisan gillar a kan sanata Dino Melaye

- Majalisar ya yi Allah wadai da harin harbe-harben bindiga da wasu ‘yan bindiga suka yi wa gidan sanatan

- Dan majalisa Solomon Ahwinahwi ya ce in ba a magance wannan al’amarin ba, toh fa, suma basu tsira ba

Majalisar wakilan Najeriya a ranar Alhamis, 27 ga watan Afrilu ta yi kira ga sufeto-Janar na ‘yan sanda Ibrahim Idris da ya gurfanar da wadanda ke bayan harin kisan gillar a kan sanata Dino Melaye.

Wannan kiran ya biyo bayan sakamakon wani motsi ta dauki nauyin da dan majalisa Herman Hermbe mai wakiltar jihar Banuwe a karkashin jam’iyyar APC ya yi.

Dan majalisar ya yi Allah wadai da harin harbe-harben bindiga da wasu ‘yan bindiga suka yi wa gidan sanata Melaye a ranar 14 ga watan Afrilu kuma suka hallaka motocinsa.

Majalisar wakilai ta yi tir da harin kisa a kan Dino Melaye

Sanata Dino Melaye a zauren majalisar dattawa

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari ccewa, duk da kiran rundunar jami'in 'yan sanda na Aiyetero Gbedde na sa’o’i 1, 'yan sanda basu zo ba har sai bayan da ‘yan bindigan sun karasa harsashin da suke tare da shi sannan suka tsira.

Dan majalisa Solomon Ahwinahwi mai wakiltar jihar Delta a karkashin jam’iyyar APC ya ce: "Ina ganin akwai bukatar mu kira Sufeto-Janar na 'yan sandan don ya zo ya bayyana wa majalisa abin da ya faru."

KU KARANTA KUMA: Ana cigiyar Salima Hussaini wanda ke yankin Mararrabar Abuja ta jihar Nassarawa

Ya ce in ba a magance wannan al’amarin ba, toh fa, suma basu tsira ba domin idan gemun dan uwarka ya kama da wuta, kaima ka yi gaggawar sama naka wuta.

Kakakin majalisar, Mista Yakubu Dogara ya umurni kwamitocin majalisa a kan yarda da dokoki da kuma al'amuran 'yan sanda da su bincike al’amarin.

Ya bukaci 'yan kwamitocin su bayar da rahoto ga majalisar cikin mako hudu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kali yadda aka kaya da rikicin takadar shaida na sanata Dino Melaye

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel