Ikon Allah: Anyi gwajin motocin tasi masu tashi a kasar Germany (Hotuna)

Ikon Allah: Anyi gwajin motocin tasi masu tashi a kasar Germany (Hotuna)

- Wani kamfani mai suna Lilium a kasar Germany ya samu nasarar gwada sanfurinsa na motocin kabu kabun masu yawo a sararin samaniya.

- Burin matasa hudun da suka bude kamfanin shi ne su saukaka harkar sifiri a duniya nan ba da dadewa ba, ta yadda kowa ma zai iya yin hayar mota mai tashi kuma akan farashin da bai kai na motocin haya ba.

Motar mai tashi dai an kirkirre ta kamar kwai, ta yadda sam ba ta da nauyi, kuma za ta iya tashi ta sauka a ko’ina. Motar ta na dauke da kananan injina guda 36, kuma ko da ace daya ya lalace, wannan ba zai hana motar aiki ba.

NAIJ.com ta samu labarin Motar za ta iya daukan fashinjoji biyar kuma za ta iya yin tafiyar kilomita 300 (kamar tsakanin Kano da Abuja) a cikin awa daya.

Ikon Allah: Anyi gwajin motocin tasi masu tashi a kasar Germany (Hotuna)

Ikon Allah: Anyi gwajin motocin tasi masu tashi a kasar Germany (Hotuna)

KU KARANTA: Ban san da zaman takardar kisan Sheikh Jafar gidana ba - Goje

Ana cajin motar da wutar lantarki ko kuma ta yi amfani da hasken rana. Ba ta fitar da kara ko hayaki.

Ko a Dubai da ke UAE, an kaddamar da irin wadannan motoci, kuma ana sa ran a cikin wannan shekara za su fara aikin sufuri a cikin birnin.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel