An yi canjaras a wasan Man City da Man Utd

An yi canjaras a wasan Man City da Man Utd

Manchester United ta ci gaba da zama a matsayinta na biyar a teburin Premier bayan wasanta da abokiyar hamayyarta Manchester City, wanda suka tashi ba ci a Etihad, amma an kori Fellaini.

United tana da maki 64 a wasa 33 yayin da Manchester City ta hudu a tebur take da maki 65, ita ma a wasa 33.

Saura minti shida a tashi daga wasan alkalin wasa ya kori Marouane Fellaini, wanda bai dade da samun katin gargadi ba saboda keta da ya yi wa Aguero, bayan da ya sake yi wa Sergio Aguero karo.

NAIJ.com ta samu labarin cewa United wadda take maki biyu a bayan Liverpool ta uku da kwantan wasa daya, ta yi wasa 24 kenan na Premier ba tare da an doke ta ba.

An yi canjaras a wasan Man City da Man Utd

An yi canjaras a wasan Man City da Man Utd

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta sake taso wani dan uwan Jonathan

Wasanta biyu daga cikin biyar da suka rage za ta yi su ne a waje, a gidan Arsenal ranar 7 ga watan Mayu da kuma gidan Tottenham ranar 14 ga watan Mayu.

Manchester City wadda za ta gama kakar farko da Pep Guardiola ba tare da kofi ba tana maki daya tsakaninta da Liverpool, amma tana da kwantan wasa daya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel