Gwamnatin Buhari zata gina kotuna a gidajen yarin kasar nan

Gwamnatin Buhari zata gina kotuna a gidajen yarin kasar nan

- Gwamnatin tarayya zata gina Kotuna a gidajen yarin dake ƙasarnan domin hanzarta gudanar da shari’a

- Ministan cikin gida Abdurrahaman Danbazau ne ya bada hasken haka yau a Abuja

- Lokacin da yake ƙaddamar da motocin aiki 239 da kuma kayayyakin amfanin gona da hukumar kula da gidajen yarin ƙasarnan ta siya.

Dambazau yace yunƙurin yana da amfani wajen rage cinkoso da ake fama dashi a yawancin gidajen yarin dake cikin biranen ƙasarnan.

NAIJ.com ta samu labarin cewa lokacin da yake bayyana rashin jin ɗaɗinsa kan yadda kaso 72 cikin 100 na waɗanda suke zaune a gidajen yarin ƙasarnan suna zaman jira shari’a ne,yace aikine mai wahalar gaske ace hukumar sai ta kai ɗaurarru sama da 50,000 zuwa kotuna daban-daban dake watse a faɗin ƙasarnan a ko wacce rana.

“Tafiyar hawainiyar da tsarin shari’a yake a ƙasar nan da kuma daɗewar da muatne suke a ɗaure kafin a fara yi musu shari’a, ya janyo cunkoson gaske a galibin gidajen yarin da ke biranen ƙasarnan”

Gwamnatin Buhari zata gina kotuna a gidajen yarin kasar nan

Gwamnatin Buhari zata gina kotuna a gidajen yarin kasar nan

KU KARANTA: Illoli 7 da shan gishiri yake yi

“Matsalar ta sake ta’azzara saboda ƙarancin ababen hawa da gidajen yarin suke dasu, daza a kai masu laifi kotu a lokutan da yadace, wanda hakan yake sa ɗaurarrun su ƙosa da kuma kokawa kan halin da suke ciki” yace

Ministan yace irin wannnan yanayi ba abune mai karɓuwa ba a gurin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari , wanda yabada umarnin siyan motocin da kuma kayan aikin gonar.

Tun farko a jawabinsa shugaban hukumar kula da gidajen yari ta ƙasa Ja’afaru Ahmad ya yabawa gwamnati kan siyan motocin da kuma kayan aikin gonar, inda yace hakan zai kawo ƙarshen rashin jin daɗin aiki da ya addabi gonakin da hukumar ta mallaka.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel