Rundunar sojin saman Najeriya a shirye ta ke ta samu taimako daga Amurka

Rundunar sojin saman Najeriya a shirye ta ke ta samu taimako daga Amurka

- Babban hafsan sojojin saman, Air Marshal Sadiq Abubakar ya ce a shirye rundunar take ta samu taimakon kayan aiki daga kasar Amurka

- Rundunar ta yaye wasu dalibai da aka koyawa sana’o’in hannu a birnin Legas

- Sadiq ya ce akwai kyakkyawar fahimtar juna tsakaninrundunar da kasar Amurka

Babban hafsan sojojin saman Najeriya ya bayyana cewar a shirye rundunar take ta samu taimakon kayan aiki musamman jiragen yaki daga kasar Amurka.

Yanzu haka dai rundunar na jiran taimakon da zarar an kammala cika sharudodin wannan cinikayya tsakanin Najeriya da kasar Amurka.

Babban hafsan sojin saman Air Marshal Sadiq Abubakar, ya bayyana hakan ne a wajen bikin yaye wasu dalibai da aka koyawa sana’o’in hannu a birnin Legas, wanda kuma ya ce suna da kyakkyawar fahimtar juna da Amurka, kuma suna taimaka musu a wurare da dama.

Rundunar sojin saman Najeriya a shirye ta ke ta samu taimako daga Amurka

Babban hafsan sojin saman Air Marshal Sadiq Abubakar

NAIJ.com ta ruwaito cewa babban hafsan ya ce yanzu haka rundunarsa ta dukufa wajen zakulo masu basira daga cikin gida, wajen amfani da abubuwan da suke sarrafawa ko kerawa domin amfanin runduanr sojan kamar yadda ya gani a wajen bikin yaye daliban da aka koyawa sana’o’in hannu a Legas.

KU KARANTA KUMA: A na samar da tabbataccen sakamako a harakar tsaro a kudancin Kaduna – Inji Hafsan tsaro

Babban hafsan ya ce cikin kayayyakin da ya gani wajen bikin akwai wasu takalma guda 2 da rundunarsa za ta iya amfani da su wajen kuratan sojoji da suke dauka, wanda hakan zai taimaka ba sai an fita waje ba don sayo takalma, da kuma zanin gado da rundunar za ta iya amfani da su.

Daliban da aka koyawa sana’o’in dai sun hada da matan da suka rasa mazajensu a fagen daga da kuma matasa da ke zaune sansanonin rundunar sojojin sama, wanda ba su da aikin yi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon yadda sojojin saman Najeriya ke yakan Boko Haram a dajin sambisa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure
NAIJ.com
Mailfire view pixel