Hukumar ‘yan sanda ta dakatar da daukar masu mukamin ASP sai...

Hukumar ‘yan sanda ta dakatar da daukar masu mukamin ASP sai...

- DIG Maigari A. Dikko ya yaba wa rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara a lokacin da ya ziyarci jihar

- Dikko ya yi wa ‘yan sandan albishir cewa hukumar ta ‘yan sanda na shirin samar wa ko wane dan sanda gida mallakar kansa

- Ya kara da cewa daga yanzu hukumar ‘yan sanda ba za ta kara daukar masu mukamin ASP ba sai wanda ya yi karatu a makarantun horar da ‘yan sanda

Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda, DIG Maigari A. Dikko ya yaba wa rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara bisa kokarinsu na maido da dabbobi da barayi suka sace guda 2,734 tare da damke gungun masu sace mutane.

DIG ya yi wannan yabon ne a lokacin da ya kawo ziyar aiki a jihar ta Zamfara.

Ya bayyana cewa wannan ziyarar albishir ce ga ‘yan sada daga sufeto janar cewa hukumarsu ta ‘yan sanda na shirin samar wa ko wane dan sanda gida mallakar kansa lokacin da zai ajiye aiki ya kasance yana da gidan kansa. A karkashin shirin ya ce kamfanoni za su samar da gidaje 500 a ko wace jiha.

Ya kara da cewa: “Hukumar ‘yan sanda na jan kunne ga wadanda suka turje a kai masu canjin wajen aiki suka ki komawa su sani cewa su ‘yan sandan kasa ne ba na jiha ba dan haka duk inda aka kai mutum dole ya tafi kuma idan mutum ya yi turje lalali zai gamu da hukunci”.

KU KARANTA KUMA: Sojoji sun hallaka yan Boko Haram 15, tare da kwato dimbin makaman yaki (Hotuna)

NAIJ.com ta ruwaito cewa, DIG ya ce daga yanzu hukumar ‘yan sanda ba za ta kara daukar masu mukamin ASP ba sai wanda ya yi karatu a makarantun horar da ‘yan sanda.

A nasa jawabi mai masaukin baki, kwamishinan ‘yan sanda na Zamfara Shaba Alkali ya bayyana jin dadinsa da ziyarar DIG Dikko kuma ya bayyana masa nasarorin da suka samu da kuma kalubalen da suke fuskanta na aiki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon yadda sojojin saman Najeriya ke yakan Boko Haram a dajin sambisa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel