Hadiza Bala Usman ta maka wani ɗan jarida kotu, ta buƙaci ya biyata naira biliyan 1

Hadiza Bala Usman ta maka wani ɗan jarida kotu, ta buƙaci ya biyata naira biliyan 1

-Shugabar hukumar NPA, Hadiza Bala Usman ta yi karar wani dan jarida saboda bata mata suna

-Hadizan tace dan jaridar yayi mata kage da gangan

Shugabar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa na Najeriya, Hadiza Bala Usman ya shigar da wani dan jarida mai suna Prince Henry Nwazuruahu Shield, tare da kamfanin sa ‘thebreakingtimes.com’ kara gaban babban kotun birnin tarayya saboda tuhumarsu da take yi da bata mata suna.

Hadiza Bala Usman ta bukaci kamfanin da dan jaridar su biyata zambar kudi naira biliyan daya a matsayin kudin fansa saboda bata mata suna da suka yi.

KU KARANTA: EFCC ta gabatar da shaidu 18 a shari’ar Sule Lamido da yayansa

Hadizan ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa data fitar a ranar Juma’a, 28 ga watan Afrilu inda tace cewa “A matsayin mu na mutane, muna da laifi idan muka sa ido yan jaridun bogi suna bata mana suna tare da gurgunta dimukradiyyar mu.”

Hadiza Bala Usman ta maka wani ɗan jarida kotu, ta buƙaci ya biyata naira biliyan 1

Hadiza Bala Usman

A ranar 22 ga watan Maris ne dai kamfanin jaridar ‘thebreakingtimes.com’ ta wallafa wani labarin karya game da Hadiza, mai taken “Yadda El-Rufai da Hadiza Bala Usman suka baiwa jigon APC cin hancin $25,000 don a nada shi mataimakin shugaban kasa”

Hadiza ta bayyana labarin a matsayin na kanzon kurege, kuma tace manufar kamfanin jaridar shine lalata mata suna, don haka ne ta kai kara kotu a kwatan mata hakkinta, kamar yadda NAIJ.com ta jiyo.

Hadiza Bala Usman ta maka wani ɗan jarida kotu, ta buƙaci ya biyata naira biliyan 1

Hadiza Bala Usman a kotu

Hadiza tace “Kafafen sadarwa na zamani ya kawo mana cigaba kwarai da gaske, amma kuna yana irin nasa nakasu, ta yadda wasu ke amfani da shi wajen cin zarafin mutane, ba tare da kwaba ba. Don haka fannin shari’a ne kadai ka iya tabbatar ma mutane hakkinsu. A yau nazo neman adalci ne.”

Hadiza ta bayyana cewa ta sha kawar da kai daga kage kagen da ake yi mata a baya, kuma tace ita mutum ce mai son gaskiya da rikon amana, kuma ba zata canza ba sakamakon wannan mukamin nata na shugaban NPA.

Daga karshe, ta shawarci kafafen watsa labarai dasu guji watsa labaran karya don neman kasuwa, kuma tayi kira ga duk wanda aka bata ma suna ta wannan kafa daya tashi ta kwato hakkinsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani irin hukunci ya dace a yanke ma barayin kudaden al'umma?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel