Kakakin majalisa ya lallasa jami’in dan sanda

Kakakin majalisa ya lallasa jami’in dan sanda

-Abun mamaki bai karewa a fagen siyasar Najeriya

-Shin saboda wani dalili kakakin majalisar dokokin jiha zai doki jami’an dan sanda

Kakakin majalisan dokokin jihar Adamawa, Kabirun Mijinyawa, ya lallasa wani dan sandan da aka sa ya yi masa gadi. Hukumar yan sanda ta tabbatar da hakan.

Wani idon shaida ya bayyanawa manema labarai a garin Yola a jiya cewa, kakakin ya fusata ne lokacin da dan sandan yayi kuka akan rashin biyansa alawus disa. Kakakin ya shake sa kuma ya faffala masa mari kafin wasu suka kwaceshi daga hannunshi.

“Wani jami’an NSCDC ne ya ceceshi inda ya fadawa kakakin cewa ya sani fa jami’an dan sanda yake duka.” Idon shaida ya bayyana.

Kakakin majalisa ya lallasa jami’in dan sanda

Kakakin majalisa ya lallasa jami’in dan sanda

Kakakin hukumar yan sanda, DSP Othman Abubakar, ya tabbatar da wannan labari inda yace kwamandan Yola na kula da al’amarin.

KU KARANTA: Buhari ya halarci Sallan Juma'a ba

Anyi kokarin tattaunawa da kakakin majalisar amma yaki daga wayarsa kuma yaki mayar da sakonni da ake tura masa.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel