'Yan Biyafara sun soki Shugaban Kasa Buhari

'Yan Biyafara sun soki Shugaban Kasa Buhari

– ‘Yan Kungiyar IPOB sun caccaki shugaba Buhari

– IPOB tace shugaba Buhari ne ya gindaya sharudan belin Nnamdi Kanu

– Wasu na ganin sharudan sun yi tsauri

Kotu ta bada damar a saki Nnamdi Kanu.

Sai dai ba a nan ta ke ba.

Don kuwa sharudan na da matukar tsauri.

Yan Kungiyar IPOB ta Biyafara sun yi tir da Shugaba Muhammadu Buhari game da shari'ar Nnamdi Kanu wanda shi ne jagoran tafiyar. Masu fafutukar sun yi Allah wadai da Shugaban Kasar su kace shi ya tsaro komai.

'Yan Biyafara sun soki Shugaban Kasa Buhari

'Yan Biyafara sun yi kaca-kaca da Buhari

Cikin sharudan belin dai sai an samu wani Bayahuden Malami da ya tsaya masa da kuma Sanatan Najeriya mai fili a Birnin Tarayya Abuja sannan kuma ba za a mika masa takardun sa ba duk don dai kar ya tsere ko ya tada wata fitina.

KU KARANTA: Uwargidan Buhari tayi abin kwarai

'Yan Biyafara sun soki Shugaban Kasa Buhari

Jagoran 'Yan Biyafara a Kotu

Kungiyar tace da wuya a cika wadannan ka'idoji da aka gindaya, ko anyi dai karshen ta za a karo kamo Nnamdi Kanu dinne kurum. Ana zargin sa da cin amanar kasa inda yake tsare tun shekarar bara a gidan kaso.

Shi dai Nnamdi KANU yace nan da lokaci kankani zai cika sharudda ya kuma fito. Nnamdi Kanu yace bai taba kin amincewa da ka'idojin belin ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An saki Nnamdi Kanu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel