Obasanjo ya bayyana dalilinsa na zaɓan Jonathan don zama mataimakin Yar’adua

Obasanjo ya bayyana dalilinsa na zaɓan Jonathan don zama mataimakin Yar’adua

- Obasanjo ya tabbatar da cewa ba Jonathan bane zabinsa na farko a tsaya takarar mataimakin Yar'adua ba

- Obasanjo yace sai daya tabbatar da lafiyar Yar'adua kafin ya tsayar da shi takara

Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana dalilin daya sanya shi zabar Goodluck Jonathan a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa tare da Umaru Musa Yar’adua a zaben shekarar 2007.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Obasanjo ya bayyana haka ne a cikin wani littafi da tsohon Kaakakin Yar’adua Segun Adeniyi ya wallafa mai taken ‘Against The Run Of Play’, inda Obasanjo yace a gaskiya yana da ra’ayin fito da tsohon gwamnan jihar Ribas ne Peter Odili, amma wasu dalilai suka sanya ya fasa dauko shi.

KU KARANTA: EFCC ta gabatar da shaidu 18 a shari’ar Sule Lamido da yayansa

Sai dai tsohon gwamnan jihar Bayelsa Alamieyeseigha y shaida a wani hira cewa “Obasanjo ya fada min cewa tunda ya fahimci da ni da Atiku muna sha’awar yin takarar shugaban kasa da mataimaki, toh lallai sai dai a bayan ransa. Tun dai har Atiku ta zabo ka a matsayin dan takararsa, toh sai nayi maganinka.”

Obasanjo ya bayyana dalilinsa na zaɓan Jonathan don zama mataimakin Yar’adua

Obasanjo da Jonathan

Cif Obasanjo a cikin littafin ya musanta batun na Alamieyeseigha, inda yace “Gaskiya ne Jonathan ba shine ra’ayina da farko ba, don zaman mataimakin Yar’adua. Peter Odili ne, amma Odili ya kasa cika wasu shikashikai, hakan ya sa na zabi Jonathan. amma kam banyi wani bincike akansa ba”

Dayake bayanin dalilin daya say a zabo Yar’adua, Obasanjo yace “Akwai damuwa game da lafiyar Yar’adua, sai batun matarsa da aka ce tana juya shi.” Amma Yar’adua ya musanta zargin da ake yi ma matarsa, inda yace yan bakin ciki ne kawai ke yayata maganar, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

“Dangane da rashin lafiyarsa kuwa, na samu sakamamon wani gwaji da aka yi mai, sai ma baiwa wani abokina likita don ya duba ya bani shawara, inda likitan ya tabbatar min da cewa Yar’adua ba shi da ciwon koda.” Inji Obasanjo.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wanene ba barawo ba a yan siyasan Najeriya?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel