Al’umar garin Chibok sun gana da kwamitin tallafawa shiyyar arewa maso gabas

Al’umar garin Chibok sun gana da kwamitin tallafawa shiyyar arewa maso gabas

- An yi wata ganawa tsakanin al’umar garin Chibok da kwamitin tallafawa wadanda rikicin Boko Haram ta shafa a shiyyar arewa maso gabas

- Ganawar ta mayar da hankali ne kan matsalolin da ‘yan yankin ke fuskanta da kuma hanyoyin da za a bi wajen tallafa musu

- Kwamitin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa don tallafawa wadanda rikicin Boko Haram ta shafa a shiyyar arewa maso gabas ya yi wata ganawa ta musamman da masu ruwa da tsaki na garin Chibok.

- Al’ummar garin sun koka kan karancin ruwan sha da rashin kyawun hanyar mota da kuma rashin makarantar sakandare

Ganawar ta mayar da hankali ne kan matsalolin da ‘yan yankin ke fuskanta da kuma hanyoyin da za a bi wajen tallafa musu. Al’ummar garin Chibok sun koka ne game da irin matsalolin da suke fuskanta da suka hada da: karancin ruwan sha da rashin kyawun hanyar mota da kuma rashin makarantar sakandare bayan da aka rufe wadda aka sace ‘yan matan Chibok.

NAIJ.com ta ruwaito cewa an tattauna ire-iren wannan matsolin da ma sauran wasu na daban. Kwamitin dai ya ce zai duba matsalolin da kuma yin alkawarin tallafawa musu dai dai gwargwado.

Batun rashin makaranta shine ya fi jawo hankulan al’ummar garin Chibok, inda suka koka da cewa anyi musu alkawarin sake gina makarantar ma tun shekaru biyu da suka gabata amma aka yi watsi da aikin.

Al’umar garin Chibok sun gana da kwamitin tallafawa shiyyar arewa maso gabas

Garin Chibok

KU KARANTA KUMA: Hukumar raya tattalin arzikin Arewa maso gabashin Najeriya

Mataimakin shugaban kwamitin Alhaji Tijjani Tumsa, ya ce dalilin taron shine duba yiwuwar ci gaba da aikin da rundunar sojan Najeriya ke kulawa da shi. Kan maganar gina hanyoyi kuma Alhaji Tijjani ya ce duk da yake damina ta karato amma za a tabbatar da ganin an kammala sauran ayyukan kafin damina ta badi.

Hakimin Chibok, Injiniya Zanna Madu Usman, ya ce suna da bukatu masu yawa amma abin da yafi damunsu shine makaranta da ruwan sha da kuma hanyoyi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon zanga-zangan 'yan matan Chibok a Legas wadanda ke hannun 'yan Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel