An shawarci gwamnatin Najeriya ta yi wa al'umma aiki da kudaden da ta kwato

An shawarci gwamnatin Najeriya ta yi wa al'umma aiki da kudaden da ta kwato

- Kungiyar kwararrun 'yan jarida reshen jihar Filato ta shawarci gwamnati da ta inganta rayuwar ‘yan Najeriya da kudaden da ta kwato a hannun barayin gwamnati

- Shugaban kungiyar ya ce hakki ne a kansu su shawarci gwamnati mai mulki domin ci gaban kasa

- Barde ya ce a tsarin mulkin Najeriya 'yan jarida suna da aikin da kasa ta dora masu

- Shugaban ya kuma ce suna murna da shirin shugaba Buhari na kawo hanyar da za'a kwato kudaden da mutane suka sace daga gwamnati

Kungiyar kwararrun 'yan jarida reshen jihar Filato ta shawarci gwamnatin tarayyar Najeriya da ta yi amfani da kudaden da ta kwato daga wadanda suka wawuresu, ta yi wa al'umma aiki domin inganta rayuwarsu.

Shugaban kungiyar kuma tsohon kwamishanan yada labarai a jihar Filato Mista Gideon Barde ya bayyana haka a matsayinsu na tsoffin 'yan jarida da suka kwashe fiye da shekaru 40 suna aikin jarida, hakki ne a kansu su dinga bibiyar tsare-tsaren gwamnati suna kuma ba da shawarwari domin ci gaban kasa.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labara, Barde ya ce a tsarin mulkin Najeriya 'yan jarida suna da aikin da kasa ta dora masu.

Ya kuma ce suna murna da shirin shugaba Buhari na kawo hanyar da za'a kwato kudaden da mutane suka sace daga gwamnati.

Ya kara da cewa kudaden da ake kwatowa ya kamata gwamnati ta duba rayuwar 'yan kasa ta kawo masu sauyi.

KU KARANTA KUMA: EFCC ta gabatar da shaidu 18 a shari’ar Sule Lamido da yayansa

Shi ma tsohon kwamishanan zabe a Najeriya Godfrey Miri ya yabawa gwamnatin tarayya wajen bankado makudan kudaden.

Miri ya kira ga hukumar EFCC ta ba da jimillar kudaden da ta karbo domin kowa ya sani.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda wani dan jam'iyyar APC mai mulki ya ce jam'iyyar na iya fadi a zabe mai zuwa a 2019

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati
NAIJ.com
Mailfire view pixel