‘Yan arewa masu ci-rani a kudu sun fara koma arewa

‘Yan arewa masu ci-rani a kudu sun fara koma arewa

- Daruruwan ‘yan arewa masaunar kudancin kasar na komawa gida domin fara shirye-shirye na aikin gona a wannan shekara da muke ciki

- Ba dukkanin yankin arewan ne daminar ta fadi ba, a wasu sassan na jihohin ba a fara alamar ruwan sama ba har yanzu

- Yayin da wadannan ‘yan ci-ranin ke kokarin tafiya gida, wasu kuma yanzu suke zuwa kudu da nufin za su fara ci-raninsu a wannan lokaci

A yanzu haka daruruwan ‘yan ci- rani wadanda suke ’yan asalin jahohin arewa da suke kudancin kasar nan sun fara tattara nasu-da-nasu suna koma arewa da nufin tarar damina domin fara shirye-shirye na aikin gona a wannan shekara da muke ciki.

Duk da kasancewa bayanai suna nunar da cewa ba a dukkanin yankin arewan ba ne daminar ta fadi ba, a wasu sassan na jihohin ba a fara alamar ruwan sama ba amma duk da hakan sun gwammace suna gida daminar ta same su a bakin gonakinsu.

KU KARANTA KUMA: Duk wanda ya iya taka rawar fim din Rariya zai samu kyauta mai girma daga Rahama Sadau

NAIJ.com ta samu labari cewa wasu daga cikin matafiyar sun bayyana dalin da ya sa suke kokarin tafiya gida saboda sun ji an ce musu an fara ruwan sama don haka za su tafi domin fara aikin gona

A yayin da wadannan ‘yan ci-ranin ke kokarin tafiya gida, sai ga wasu kuma sun baro arewan zuwa kudu da nufin za su fara ci-raninsu a wannan lokaci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon rikicin Ile-Ife tsakanin mazauna hausawa 'yan arewa da kuma yorubawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure
NAIJ.com
Mailfire view pixel