Shugaba Buhari ya maidawa Jonathan kakkausan raddi

Shugaba Buhari ya maidawa Jonathan kakkausan raddi

– Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya maidawa Jonathan martani

– Buhari yace da rashin gaskiya yake fada ba da Jonathan ba

– Tsohon shugaba Jonathan yace shi ake yaka da iyalin sa kurum

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya maidawa Jonathan martani.

Buhari yake cewa idan har Jonathan yana jin ana yi masa ba daidai ba to ya garzaya kotu.

Wannan magana ta fito ne ta bakin mai magana da bakin Shugaban kasar watau Femi Adesina.

Shugaba Buhari ya maidawa Jonathan kakkausan raddi

Idan Jonathan na da gaskiya ya yi shiru babu abin da zai faru da shi Inji Buhari

Femi Adesina ya maidawa wannan amsa ne ga tsohon shugaban kasar Dr. Goodluck Jonathan bayan ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari na nema ya ci mutuncin iyalin sa da sunan yaki da sata a kasar.

KU KARANTA: Abin da ya sa nayi wuyar gani-Buhari

Shugaba Buhari ya maidawa Jonathan kakkausan raddi

Da rashin gaskiya nake fada ba Jonathan ba - Shugaban kasa Buhari

Jonathan yayi kaca-kaca da yakin da shugaba Buhari yake yi, yace da dangin sa kadai ake fada. Sai dai Adesina yace babu wani da ya fi karfin doka a Kasar. Femi Adesina yace bai kamata wani ya tsorata da yakin idan har yana da gaskiya ba.

Yanzu haka Hukumar EFCC ta kara daura sababbin laifuffuka a kan na da kan wani Danuwan Shugaba Jonathan, Aziola Robert da matar sa Stella.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda ya kamata a rika hukunta masu laifi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel