Saura kiris a kammala aikin kasafin kudi-Inji Sanata Lawan

Saura kiris a kammala aikin kasafin kudi-Inji Sanata Lawan

– Kawo yanzu babu kasafin kudi a Najeriya

– Majalisa ba ta tabbatar da kasafin da shugaba Buhari ya aika ba

– Sanata Ahmed Lawan ya tabbatar da cewa ana daf da kammala aikin

Dazu NAIJ.com ke rahoto cewa har yanzu babu kasafin kudi a Najeriya.

Don kuwa ga shi har yau ana shirin shiga watan 5 Majalisa ba ta tabbatar da kasafin da aka tura ma ta ba.

A bara ma dai sai da aka kai wannan lokaci kafin a sa hannu a kasafin.

Saura kiris a kammala aikin kasafin kudi-Inji Sanata Lawan

Shugaban kasa tare da Shugaban Majalisa

Sanata Ahmed Lawan ya tabbatar da cewa suna kokarin ganin an kammala aikin da ya rage zuwa mako mai zuwa sai dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu. Majalisar tayi alkawarin hakan zuwa karshen watan Afrilu.

KU KARANTA: Dole a gyara gidan yari Inji Honarabul Jagaba

Saura kiris a kammala aikin kasafin kudi-Inji Sanata Lawan

Ana rattaba hannu kan kasafin kudi

Ahmad Lawan ya bayyana haka bayan ya fito daga fadar shugaban kasa Buhari inda ya gana da ‘Yan jarida. Haka kuma zuwa mako mai zuwa dai za a tantance Ministocin da shugaban kasa ya aika Majalisar.

Shugaban kwamitin kasafin na Majalisar Dattawa Sanata Danjuma Goje yace ‘Yan Sanda sun yi awon gaba da takardun kasafin makon baya da suka kai wani samame gidan sa. Sai dai ‘Yan Sanda sun karyata wannan.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda za a kama barayi a Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel