Osinbajo da gwamnonin Najeriya sun ɗauki matakan kawar da cutar shan inna

Osinbajo da gwamnonin Najeriya sun ɗauki matakan kawar da cutar shan inna

- Gwamnatin tarayya zata baiwa gwamnoni tallafin kudi don yaki da cutar shan inna

- Gwamnoni sun yi alkawarin jaircewa don yakar cutar

Mataimakin shugaban kasa Frafesa Yemi Osinbajo ya bayyana manufar gwamnatin tarayya na magance cutar shan inna daga Najeriya gaba daya.

Osinbajo ya bayyana haka ne a wata ganawa da yayi da gwwamnonin Najeriya akan yadda za’a shawo kan cutar, taron ya gudana ne a fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis 27 ga watan Afrilu.

KU KARANTA: Shugaban jam’iyyar APC ya gana da gwamnoninsa

An samu sake bullar cutar a yankin Arewa maso gabas sakamakon rikicin ta’addanci daya dabaibaye yankin, musamman a kauyukan da aka kwato kwanan nan.

Osinbajo da gwamnonin Najeriya sun ɗauki matakan kawar da cutar shan inna

Osinbajo da gwamnonin Najeriya

Mataimakin shugaban kasan ya bukaci gwamnoni dasu mayar da hankali ga yakar cutar shan inna a jihohinsu yadda ya kamata, sa’annan ya tabbatar musu cewar gwamnatin tarayya zata bude wuraren alluran riga kafi a kauyuka.

Osinbajo da gwamnonin Najeriya sun ɗauki matakan kawar da cutar shan inna

Osinbajo da gwamnonin Najeriya

Osinbajo ya baiwa gwamnonin tabbacin cewa gwamnati zata sakar musu kudaden da aka ware na yakar cutar shan inna da zarar majalisa ta amince da kasafin kudin bana. Shima ministan lafita Farfesa Isaac Adewole yace gwamnati tana bin duk hanyoyi da suka kamat wajen ganin an samu nasarar kau da shan inna.

Osinbajo da gwamnonin Najeriya sun ɗauki matakan kawar da cutar shan inna

Osinbajo da gwamna Tambuwal

Sarauknan gargajiya, hukumar kula da lafiya ta majalisar dinkin duniya, WHO, shuwagabannin addinai duk sun samu halartan taron, inji rahoton NAIJ.com.

Osinbajo da gwamnonin Najeriya sun ɗauki matakan kawar da cutar shan inna

Gwamnoni yayin taron

A nasa jawabin, shugaban gwamnonin Najeriya, Abdul Aziz Yari ya yaba ma kokarin da gwamnati keyi na ganin an kawar da cutar shan inna, kuma yace gwamnoni m zasu cigaba da bada goyon baya ga kokarin gwamnatin .

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin akwai dan siyasar da baya satar kudi?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja
NAIJ.com
Mailfire view pixel