Sheikh Ja'afar: Ku fayyace gaskiya 'yan sanda - Goje

Sheikh Ja'afar: Ku fayyace gaskiya 'yan sanda - Goje

- Sanata Danjuma Goje ya bukaci rundunar 'yan sandan kasar, ta fito ta bayyana gaskiya kan mutanen da suka kashe Sheikh Ja’afar

- Danjuma Goje ya ce ya yi wannan kira ne saboda yadda ake kokarin goga masa kashin kaji

Sanata Danjuma Goje ya bukaci rundunar 'yan sandan kasar, ta fito ta bayyana gaskiya kan mutanen da suka kashe malamin addinin musulunci Sheikh Ja'afar Muhd Adam.

Shugaban kwamitin kasafin kudi a majalisar dattijan Najeriya, sanata Danjuma Goje ya ce ya yi wannan kira ne saboda yadda ake kokarin goga masa kashin kaji.

Ya ce: "Amma na hakikance ba ni da wani alaka da takardar da ta shafi wai yadda Shekarau ya tsara halaka marigayi Sheikh Ja'afar."

Sheikh Ja'afar: Ku fayyace gaskiya 'yan sanda - Goje

Sanata Danjuma Goje ya bukaci yan sanda da su fayyace gaskiya kan mutuwar Ja'afar

A cewarsa “Yan sanda, kamata ya yi su fi kowa shinin wa ya kashe Sheikh Ja'afar. Wa ya tsara."

Sanata Goje na mayar da martani ne a kan bayanin da rundunar 'yan sandan ta yi game da kudi da takardun da ta gano yayin samamen da ta kai gidansa.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar yan fensho na kasa sun karrama Gwamnoni 6

'Yan sanda sun ce a cikin takardun akwai wani fayel mai dauke da rubutu a kan kashe Sheikh Ja'afar Adam a Kano, har ma sun ambaci sunan tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau.

Tuni dai wannan bayani ya janyo gagarumin ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta a tsakanin 'yan Najeriya.

NAIJ.com ta tuna cewa a ranar 13 ga watan Afrilun 2007 ne wasu mutane suka harbe fitaccen malamin addinin musulunci yayin sallar asubah a Kano.

Danjuma Goje dai ya ce bayanin 'yan sanda wani yunkuri ne kawai na shafa masa kashin kaji "don a cuce ni."

Ya ce yana wannan magana ce don ya lura da yadda ake son bata masa suna. "A manna mini abin da ba gaskiya ne a jikina ba."

Ya zuwa yanzu dai ba a ji martanin da tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya mayar game da batun ba.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan ma dai wani gwamnan ne da ya tuka matar sa da kan sa.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC
NAIJ.com
Mailfire view pixel