Majalisa ta kusa tantance Ministocin da Buhari ya tura

Majalisa ta kusa tantance Ministocin da Buhari ya tura

– Makon gobe Majalisa za ta tantance sababbin Ministoci

– Haka kuma Majalisa ba ta tabbatar da kasafin da shugaba Buhari ya aika ba

– Jagoran Majalisar Sanata Ahmed Lawan ya tabbatar da wannan

Kuna da labari daga NAIJ.com cewa Sanata Ahmed Lawan ya tabbatar da cewa suna kokarin ganin an kammala aikin da ya rage na kasafin kudi zuwa mako mai zuwa.

Majalisar tayi alkawarin hakan zuwa karshen watan Afrilu a baya.

Har yanzu dai shiru ka ke ji babu labari.

Majalisa ta kusa tantance Ministocin da Buhari ya tura

Marigayi James Ocholi ya mutu a ofis

Majalisar Dattawa ta kuma tabbatar da cewa a makon gobe za a tantance sababbin Ministocin da shugaban kasa ya tura masu. Wata guda kenan da shugaba Buhari ya aika sunayen Farfesa Ikani Ocheni da Sulaiman Hassan.

KU KARANTA: Uwargidan shugaba Buhari tayi abin burgewa

Majalisa ta kusa tantance Ministocin da Buhari ya tura

Amina Mohammed ta bar kujerar ta

Ahmad Lawan ya bayyana haka ne bayan ya fito daga fadar shugaban kasa Buhari inda ya gana da ‘Yan jarida a fadar Aso Villa. Sanatan yace dole a samu hadin kai tsakanin Sanatoci da shugaban kasa.

A bara dai Barista James Ocholi ya rasu a hadarin mota inda kuma Ministan muhalli Amina J. Mohammed ta samu matsayi a Majalisar Dinkin Duniya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

APC na cikin matsala Inji 'Dan ta

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel