An gurfanar da mutane 3 akan laifin satan akuyoyi 9 a Osun

An gurfanar da mutane 3 akan laifin satan akuyoyi 9 a Osun

An gurfanar da wasu masu laifi 3 ranan Alhamis a kotun majistaren Ifetedo da ke jihar Osun kan laifin satan akuyoyi 9.

Lauyan, Insp James Obaletan ya bayyanawa kotu cewa abubuwan zargin - Ojo Omonigbehin, 68; Sunday Ogunlana, 45 da Adewale Olafusi, 37 – sun aikata laifin ne ranan 23 ga watan Afrilu.

Obaletan yace kowanne daga cikinsu ya saci akuya 3 a titin Oke-Soka, Ifetedo a karamar hukumar Ife ta kudu a jihar Osun. an kara da cewa kowani akuya zai kai N75,000.

Yace akuyoyin na Mrs Felicia Adedire, Mrs Faith Idafe da Mrs Esther Oluwasaanufunmi.

An gurfanar da mutane 3 akan laifin satan akuyoyi 9 a Osun

An gurfanar da mutane 3 akan laifin satan akuyoyi 9 a Osun

Amma abubuwan zargin sun ce basu aikata laifin ba. Lauyansu, Mr. Ola Ibrahim, yayi kira ga kotun ta basu beli.

Alkaliyar majistaren, Iyabo Salami, ta basu belin N50,000 da kuma kadara mai irin kudin belin.

KU KARANTA: Saraki ya kai ziyara ga maras lafiya

Iyabo Salami tace wanda zai tsaya musu sai ya kasance ma’aikanci ne kuma ya gabatar da takardan shaidan biyan haraji na shekara 3.

Ta dakatad da karan zuwa ranan 3 ga Mayu inda za’a sake ambaton zancen kuma tace a garkamesu a kurkukun Ile-Ife har sai sun cika ka’idojin belin.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel