Dakataccen sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya ki amsa gayyatar majalisa

Dakataccen sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya ki amsa gayyatar majalisa

- Babachir Lawal ya ki amsa gayyatar da kwamitin majalisa ta yi masa a ranar Alhamis, 27 ga watan Afrilu

- Kwamitin majalisar ta baiwa tsohon sakataren wa'adi zuwa karfe 12pm na rana

Dakataccen sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya ki amsa gayyatar da kwamitin majalisa ta yi masa domin amsa tambayoyi kan zargin karkatar da milyan 200 na sharar fili a yankin arewa maso gabas

Kwamitin dai ya baiwa tsohon sakataren wa'adi zuwa karfe 12pm na rana, a ranar Alhamis, 27 ga watan Afrilu idan bai gurfana a gabanta ba, kafin ta dauki matakin da ya dace a kansa.

Makon da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatarda da Babachur David Lawal kuma ya kafa wata kwamiti a karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo domin binciken sakataren da shugaban hukumar leken asirin kasar.

KU KARANTA KUMA: Abin da kwamitin Osinbajo na bukata daga majalisar dattijai a kan binciken Babacir Lawal

NAIJ.com ta ruwaito cewa, yayin da aka fara wannan bincike har yanzu ‘yan Najeriya na ganin akwai wasu jami’an gwamnatinsa da dama da ake zargin da cin hanci, cikinsu har da, wanda ake zargi da mallakar manyan gidaje na sama da dala miliyan 1.5 a birnin Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa. Haka nan kuma, ga batun badakalar MTN, lamarin da yanzu haka yan kasar ke tsokaci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari daga Landon

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel