Madalla: Naira na cigaba da daraja

Madalla: Naira na cigaba da daraja

– Darajar Naira na cigaba da tashi a kasuwa

– CBN na cigaba da sakin makudan daloli

– Shugaban yan canji Aminu Gwadabe ya yabawa CBN

A jiya mun samu cewa Naira na kara tashi a kasuwar canji.

CBN na cigaba da sakin makudan miliyoyin domin ma su bukata.

CBN ta saki kudi har dala miliyan $246.

Madalla: Naira na cigaba da daraja

Naira na kara daraja a kasuwa

A farkon makon nan Dalar tana kan N390 idan kuna tare da NAIJ.com. Sakin kudin da CBN ke yi ne ya kai har Dalar ta dan fadi a kasuwa. Haka kuma Naira ta daga kan Dalar Pounds sterling ta Ingila da N5 bayan an saida ta a kan N495 makon jiya.

Jiya NAIJ.com ta rahoto cewa CBN ta saki Dala Miliyan 246.2 a Ranar Litinin. A karshen makon jiya dai an saida Dala kan N385 wanda ya daga a farkon makon nan zuwa N390 a hannun ‘yan kasuwa. Yanzu haka dai Dalar ta koma N382 inda aka samu ragi.

KU KARANTA: An karrama wasu Gwamnoni 6; Ka ji dalili

Madalla: Naira na cigaba da daraja

Babban bankin Najeriya CBN

Shugaban 'Yan canji Aminu Gwadabe ya yabawa bankin CBN wajen sakin makudan miliyoyi a kasuwa. Gwadabe yace hakan zai yawaita Dalar Amurka a kasar ya kuma hana badakalar da ke cikin kasuwar.

Babban bankin kasar nan watau CBN ya bayyana lokacin da Najeriya za ta fita daga cikin matsin da ta shiga na durkushewar tattalin arziki. Gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ya bayyana haka kamar yadda mu ka samu labari.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yanayin farashin kayan kasuwa a Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel