Ba wajibi bane Buhari ya jagoranci ganawar majalisan zantarwa ba – Gwamnonin APC

Ba wajibi bane Buhari ya jagoranci ganawar majalisan zantarwa ba – Gwamnonin APC

-Gwamnonin jam’iyyar APC sun gana a Abuja tare da shugabanni jam’iyyar APC

-Sunce rashin halartan taron FEC da Buhari yayi baa bun damuwa bane

Gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), sunyi ittifakin cewa ba wajibi bane shugaba Muhammdu Buhari ya jagorancin taron majalisar zantarwa ba.

Gwamna Nasri El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana wannan ne ranan Laraba a Abuja, yayinda yake magana da manema labarai bayan ganawar gwamnonin jam’iyyar da shugabannin jam’iyyar APC na kasa.

Yace kundin tsarin mulkin Najeriya ta baiwa mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, daman shugabantan irin wannan ganawa idan shugaban kasa baya nan.

Ba wajibi bane Buhari ya jagoranci ganawar majalisan zantarwa ba – Gwamnonin APC

Ba wajibi bane Buhari ya jagoranci ganawar majalisan zantarwa ba – Gwamnonin APC

Yace: “ Bamu damu da ba amma duk da hakan muna kira gay an Najeriya su cigaba da addu’an lafiya ga shugaba Buhari.”

“Ko ni da ked an dan shekarar 57, ina zuwa ganin likita.”

Kana kuma yayi watsi da maganan cewa akwai Baraka cikin jam’iyyar APC inda ya jaddada cewa jam’iyyar na nan da shugabanninta, babu wani rikici.

EL-Rufai yayi bayanin cewa jam’iyyar na fuskantar matsalan kudi a yanzu saboda bata dogara da kudin jama’a kamar sauran jam’iyyu ba.

KU KARANTA: Da yiwuwan Nnamdi Kanu ya karashe rayuwa a kurkuku

Game da cewarsa, masu daukan nauyin jam’iyyar wasu masu zaman kansu ne kawai wadanda kuma sukeyi kafin ta ci zabe.

Ya kara da cewa shugabancin jam’iyyar na shirye da komawa wurin wadanan masu daukan nauyinta domin bukatan kudi.

El-Rufai ya cewa dukkan gwamnonin da ke ganawar sun mara goyon baya da biyayyansu ga shugabancin jam’iyyar kuma sunyi alkawarin ganawa da kwamitin aikin jam’iyyar kowani wata.

Yace za’a zabi wani rana ta musamman domin ganawar shugabannin jam’iyyar da gwamnonin.

Shugaban jam’iyyar Chief John Odigie-Oyegun, ya yabawa gwamnonin akan halartan ganawar duk da cewa ba’a sanar da su da wuri ba.

Gwamnonin APC 20 ne suka halarci ganawar.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel