Fasa-ƙwaurin shinkafa yana durkusar da kasuwancin na gida

Fasa-ƙwaurin shinkafa yana durkusar da kasuwancin na gida

- Gwamnatin Najeriya ta ɓullo da matakai don bunƙasa noman shinkafa a cikin gida

- Masu fasa-kwauri da hada baki da jami`an kwastam wajen satar shiga da shinkafa ƙasar

- Masu sarrafa shinkafar da kasuwancinta sun ce suna fuskantar barazanar

- Masu shinkafar sun koka kuma da cewa rashin cinikin ya sa farashin shinkafar na faɗuwa

Masana'antun shinkafa a Najeriya sun koka a kan koma-bayan kasuwa da shinkafar da suke sarrafawa a cikin gida take fuskanta saboda fasa-ƙwaurin ta ƙasashen waje da ake yi.

Sun bayyana fargabar cewa burin gwamnatin ƙasar na wadata Najeriya da shinkafa a nan kusa ka iya zama mafarki, inda suka yi zargin cewa masu fasa-kwauri da hada baki da jami`an kwastam wajen satar shiga da ita ƙasar.

Wannan lamari dai a cewarsu, ya sa kasuwar shinkafar gida ta faɗi, abin kuma da ke tilasta rufe masana`antun.

KU KARANTA: Yadda El-Rufai da Saraki suka hana ni zama mataimakin shugaban kasa - Tinubu

Gwamnatin Najeriya a baya-bayan nan ta ɓullo da matakai iri daban-daban don bunƙasa noman shinkafa a cikin gida.

Daga ciki har da bai wa manoma da masu masana'antun sarrafa shinkafa kariya ta hanyar taƙaita shigar da ita daga ƙasashen waje.

Sai dai, a baya bayan nan masu sarrafa shinkafar da kasuwancinta sun ce suna fuskantar barazanar da ka iya gurgunta musu sana'a.

Hukumar Kwastan ta Najeriya a nata bangaren ta ce tana da labarin fasa-ƙwaurin shinkafar amma bai yi munin da zai sa shinkafar waje ta mamaye kasuwannin kasar ba

Hukumar Kwastan ta Najeriya a nata bangaren ta ce tana da labarin fasa-ƙwaurin shinkafar amma bai yi munin da zai sa shinkafar waje ta mamaye kasuwannin kasar ba

Injiniya Nazifi Ilyasu shi ne kakakin kungiyar masu sarrafa shinkafa ta Najeriya kuma ya shaida cewa yanzu kasuwancin shinkafa ta cikin gida, ba ya tafiya.

Ya kuma yi zargin cewa: ''Ana shigo shinkafar kasashen waje sosai ta wasu kan iyakokin Najeriyar, tana neman ta taɓa harkar masana'antunmu.''

Masu shinkafar dai sun koka kuma da cewa rashin cinikin ya sa farashin shinkafar na faɗuwa.

NAIJ.com ya tara cewa akwai masana'antun sarrafa shinkafa da dama da suka rufe aiki a yankin jihar Kano.

KU KARANTA: CBN ta bayyana lokacin da tattalin arzikin Najeriya zai dawo daidai

Amma kuma a ɓangaren 'yan kasuwa sun ce rangwamen farashi ne ke sa shinakafar waje kashewa ta gida kasuwa.

Alhaji Uba Zubairu Yakasai shugaban kasuwar kwanar Singer ta Kano, ya ce shinkafar gida ta fi ta waje tsada shi ya sa ake sayen ta fiye da ta gida.

Ya kuma ce ta gidan idan farashinta ya yi ƙasa babu abin da zai sa mutane su sayi ta waje.

Hukumar Kwastan ta Najeriya a nata bangaren ta ce tana da labarin fasa-ƙwaurin shinkafar amma bai yi munin da zai sa shinkafar waje ta mamaye kasuwannin kasar ba.

Ta kuma musanta cewa ana haɗa baki da wasu jami'anta wajen shigar da shinkafar daga waje.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wannan NAIJ.com bidiyo na duba farashin abubuwa a kasuwa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC
NAIJ.com
Mailfire view pixel