Jonathan ya ji tsoron cewa Buhari zai kai ji kurkuku ko ya kashe shi - Obasanjo

Jonathan ya ji tsoron cewa Buhari zai kai ji kurkuku ko ya kashe shi - Obasanjo

- Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya ji tsoron cewa magajin sa, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tura sa gidan yari

- Furucin Obasanjo na kunshe ne a cikin wani littafi da shugaban sashin tantance rubutu na ThisDay, Segun Adeniyi ya rubuta

- Ya ce ba wai Jonathan na tsoron rayuwar sa bane amma sai dai abunda shugaba Buhari ka iya yi masa

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya ji tsoron cewa magajin sa, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tura sa gidan yari.

Ikirarin Obasanjo na kunshe ne a cikin wani littafi da shugaban sashin tantance rubutu na ThisDay, Segun Adeniyi ya rubuta.

Tsohon shugaban kasar ya yi ikirarin cewa ba wai Jonathan na tsoron rayuwar sa bane amma sai dai abunda shugaba Buhari ka iya yi masa.

KU KARANTA KUMA: Yadda El-Rufai da Saraki suka hana ni zama mataimakin shugaban kasa - Tinubu

A cewar Obasanjo, “Na yarda da cewan tsoron shugaban kasa ba wai na rayuwar sa a kujerar mulki bane, saboda shi da ni mun sha zama muyi magana a kan wadannan abubuwa biyu sosai.

“Na amince da cewan tsoron shugaban kasa ya ta’allaka ne a kan mutumin da yake kallo a matsayin magajin sa, wato Janar Buhari.

“Na san cewa mutane zasu dunga fada masa cewa Buhari mutun ne mai wuyan sha’ani; zai yaki rashawa kuma shi (Jonathan) na iya karewa a gidan yari idan ba kabari ba.”

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani tsohon soja ya shawarci gwamnatin tarayya da ta sasanta da kungiyar IPOB.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel