Shin Nnamdi Kanu na iya karbar belin da aka saka masa?

Shin Nnamdi Kanu na iya karbar belin da aka saka masa?

– Kotun Tarayya ta bada belin jagoran Biyafara Nnamdi Kanu

– Sai dai fa da kamar wuya a iya cika ka’idojin da aka gindaya

– Nnamdi Kanu dai ya dade a tsare

Daga karshe dai Allah yayi Kotu ta bada belin Nnamdu Kanu.

Kanu wani jagora ne na tafiyar Biyafara sai dai ka’idojin da mai shari’a Binta Nyako ta zuba suna da tsauri kwarai da gaske.

Watakila hakan ma ta sa Kanu yace sam bai yarda ba.

Shin Nnamdi Kanu na iya karbar belin da aka saka masa?

Nnamdi Kanu a gidan rediyon Biyafara

Cikin ka’idojin da NAIJ.com ta kawo maku su a baya akwai dai cewa sai an samu wani Bayahuden Malami da ya tsaya masa da kuma Sanatan Najeriya mai gida a Birnin Tarayya Abuja sannan kuma ba za a mika masa takardun sa ba.

KU KARANTA: Wani Gwamna ya buge da zaman yari

Shin Nnamdi Kanu na iya karbar belin da aka saka masa?

Masu neman kasar Biyafara

Wannan dai zai hana Kanu tserewa ko ina ko da ma can shugaba Buhari ya taba bayyana cewa Nnamdi Kanu na da fasfo har biyu kuma ya shigo Najeriya ba tare da ka’ida ba. Ana zargin Kanu da kokarin cin amanar kasa da sauran manyan laifuffuka.

Dole dai Nnamdi Kanu ya bayyana a gaban Kotu ranar shari’ar sa duk da yayi ikirarin rashin lafiya. Haka kuma an haramta masa zama cikin taron Jama’a da kuma yin hira da ‘yan jarida ko tada wani taro.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kotu ta saki Nnamdi Kanu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel