A na samar da tabbataccen sakamako a harakar tsaro a kudancin Kaduna – Inji Hafsan tsaro

A na samar da tabbataccen sakamako a harakar tsaro a kudancin Kaduna – Inji Hafsan tsaro

- Hafsan tsaro na kasar ya ce, sojoji na musamman na samar da tabbataccen sakamako a harakar tsaro a yankin kudancin Kaduna

- Ya ce`Operation Harbin Kunama ll, da aka kaddamar ta kwace makamai daban-daban a yankin a cikin mako daya

Hafsan tsaro na kasar (CDS), Janar Abayomi Olanisakin, a ranar Talata, 26 ga watan Afrilu ya ce, sojoji na musamman na samar da tabbataccen sakamako a harakar tsaro a yankin kudancin Kaduna.

Hafsan tsaron ya shaida wa manema labarai a Kaduna cewa `Operation Harbin Kunama ll, da aka kaddamar da mako daya da ta gabata ta kwace makamai daban-daban a yankin.

CDS ya ce sojojin na amfani da hanyoyin magance batun rashin tsaro a yankin ciki har da fashi da kuma barayin shanu.

A na samar da tabbataccen sakamako a harakar tsaro a kudancin Kaduna – Inji Hafsan tsaro

Hafsan tsaro na kasar (CDS), Janar Abayomi Olanisakin

A cewar shi, shugabannin gargajiya, addinai da kuma siyasa duk suna da hannu a cikin kokarin ganin cewa an tabbatar da zaman lafiya a yankin.

KU KARANTA KUMA: Yadda wani soja ya sanya ɗan saurayi ‘kamo kifin oga’ (Bidiyo/hoto)

NAIJ.com ta ruwaito cewa hafsan tsaron na Kaduna ne don kaddamar da wata dakin taron mai mutane 1,000 a kwalejin kimiya na sojojin sama wato ‘Air Force Institute of Technology’.

Ya yaba wa babban hafsan sojan sama, Air Marshall Sadiq Abubakar domin hangen nesa da kuma abar koyi shugabanci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon yadda sojojin saman Najeriya ke yakan Boko Haram a dajin sambisa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel