Ahmed Musa da budurwar sa Juliet sun saki hotunan aurensu

Ahmed Musa da budurwar sa Juliet sun saki hotunan aurensu

- Hotunan da suka billo ya nuna cewa Ahmed Musa ya shirya auren sabuwar mata a yanzu

- Dan wasan na Super Eagles ya saki hotunan aurensa tare da amaryar ta sa

- Rahotanni sun kawo cewa dan wasan zai yi auren a watan Yuli

Dan wasan Super Eagles Ahmed Musa ya shirya auren mata ta biyu kamar yadda hotunan auren sa tare da sabuwar matar Juliet ya yadu a yanar gizo.

Ku tuna cewa dan wasan ya samu rikici da matar sa ta farko Jamila a kwanan nan a gidan sa dake Landan sannan kuma yan sandan Landan suka kama shi.

NAIJ.com ta ruwaito cewa mahaifiyar ‘ya’yan Ahmed Musa guda biyu ta tada hankalinta kan shawarar da mijinta ya yanke na auro mata ta biyu.

Ahmed Musa da budurwar sa Juliet sun saki hotunan aurensu

Ahmed Musa da budurwar sa Juliet sun saki hotunan aurensu

KU KARANTA KUMA: Yadda El-Rufai da Saraki suka hana ni zama mataimakin shugaban kasa - Tinubu

Ana ta rade-radin cewa dan wasan ya saki matar sa Jamila, uwar ‘ya’yansa guda biyu, a kokarin san a kawo sabuwar masoyiyarsa da ta fito daga Calabar.

Ana sa ran cewa za’a gudanar da auren ne a farkon satin watan Yuli na 2017 a jihar Lagas.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon yan wasa a lokacin da suke shirin zuwa wani wasa.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel