Zanga-zangar ma’aikatan hukumar tashoshin ruwan Najeriya

Zanga-zangar ma’aikatan hukumar tashoshin ruwan Najeriya

- Ma’aikatan hukumar tashoshin jiragen ruwan Najeriya da hukumar ta yi watsi sun yi zanga-zangar lumana a gaban ofishin hukumar da ke Legas

- An gudanar da wannan zanga-zanga ne domin jan hankalin hukumomin tashoshin jiragen ruwan, musamman ma shugabar hukumar

- A cewar masu zanga-zangar sun fito ne domin neman hakkinsu a hannun ma’aikatar NPA kusan shekaru 10 bayan sun kammala ‘daukar darasi a hukumar

- Hukumar ta ce za ta duba wannan kuka da masu zanga-zangar suka gudanar

Daruruwan ma’aikatan hukumar tashoshin jiragen ruwan Najeriya ne da hukumar ta yi watsi da su, suka gudanar da zanga-zangar lumana a gaban ofishin hukumar da ke Legas, domin kira ga hukumar da kuma gwamnatin Najeriya na maida su bakin aiki da kuma biyansu hakkokinsu.

NAIJ.com ta ruwaito cewa, ma’aikatan sun gudanar da zanga-zangar lumana ne domin nuna rashin jin dadinsu da halin ko in kula da hukumar tashoshin ruwan Najeriya ke nuna musu, kusan shekaru 10 bayan sun kammala ‘daukar darasi a hukumar tashohin jiragen ruwan.

An gudanar da zanga-zangar ne domin jan hankalin hukumomin tashoshin jiragen ruwan, musamman ma shugabar hukumar Mallama Hadiza Bala Usman, na ganin ta ‘dauke su aiki maimakon sabbin ma’aikata da yanzu rahotanni ke cewa hukumar na ganawa da su domin ‘daukarsu aiki, duk kuwa da umarnin wata babbar kotun tarayya da ke Legas da kuma majalisar tarayyar ta bayar na cewa a dakatar da ‘daukar sabbin ma’aikatan, har sai an saurari kukan ma’aikatan da tun farko aka ‘dauka tare da horas da su.

KU KARANTA KUMA: Rundunar yan sanda ta bankado takardun dake alakanta Shekarau da kisan Sheikh Ja'afar

A cewar daya daga cikin masu zanga-zangar ya ce sun fito ne domin neman hakkinsu a hannun ma’aikatar NPA, biyo bayan kwashe shekaru 10 da aka yi duk da cewa sun mika kukansu duk inda ya kamata, amma shuru babu labari.

Manajan hulda da jama’a ta hukumar ta yi jawabi ga masu zanga-zangar, inda ta ce tayi imanin cewa kasancewar shugabar hukumar da ta ke ‘yar rajin kare hakkin bil Adama ce, za ta duba wannan kuka da masu zanga-zangar suka gudanar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon zanga-zangar cika shekaru biyu ba tare da 'yan matan Chibok ba

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel