2017: Har yanzu babu kasafin kudin wannan shekarar a Najeriya

2017: Har yanzu babu kasafin kudin wannan shekarar a Najeriya

– Idan ba ayi sa’a ba dai wannan shekarar babu kasafin kudi a Najeriya

– Har yau Majalisa ba ta tabbatar da kasafin da aka tura ma ta ba

– Sanata Danjuma Goje yace ‘Yan Sanda sun yi awon gaba da takardun

Da alamu dai idan ba ayi sa’a ba bana babu kasafin kudi a Najeriya kamar yadda NAIJ.com ke lura da abubuwa.

Don kuwa ga shi har yau ana shirin shiga watan 5 Majalisa ba ta tabbatar da kasafin da aka tura ma ta ba.

Haka dai aka yi ta wannan dodo-ri-don a bara.

2017: Har yanzu babu kasafin kudin wannan shekarar a Najeriya

Babu kasafin kudi bana a Najeriya?

Shugaban kwamitin kasafin na Majalisar Dattawa Sanata Danjuma Goje yace ‘Yan Sanda sun yi awon gaba da takardun kasafin makon baya da suka kai wani samame gidan sa. Danjuma Goje dai tsohon Gwamna ne.

KU KARANTA: Majalisar Dattawa ta gayyaci Babachir

2017: Har yanzu babu kasafin kudin wannan shekarar a Najeriya

Har yau Majalisa ba ta tabbatar da kasafin da Shugaban kasa ya tura ma ta ba tun bara

Sai dai ‘Yan Sanda sun ce sam ba su dauki takardun kasafin kudin kasar ba, illa dai wasu makudan kudi har da kasar waje da su ka samu cikin gidan. Jami’an ‘Yan Sanda su kace idan har ta kai su na iya fito da bidiyo domin wanke kan su.

Kwanaki Bukola Saraki ya bayyana cewa zuwa karshen watan Afrilu Majalisa za ta amince da kasafin kudin banan sannan su kuma aikowa shugaban kasa aikin da aka yi. Yace shirin su shi ne su kammala aikin zuwa karshen watan Maris wanda ga shi har ya zo karshe.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yan kasuwa na bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel